
Sheikh Yakub Yahya Katsina.
Daga --Idishia Jos.
Imam Khumain yana cewa Allah yana suturta mutum kuma yana kawar da kai amma idan fa ka taka wannan jan layin na Allah to, komai zai bayyana za'a ganka a rana kamar yadda mutane suke fada.
Al'umman musulmai su suka fara samun izza amma da suka taka layin Allah sai abin ya juya musu. Sannan kuma kullum mu tuna komai yana hannun Allah, amma Allah yana cewa ku cika alkawari ni kuma na cika nawa. Cika alkawari Allah gaba da 'yan'uwa to yaushe ne masu yin wasu abubuwa makamantan haka Allah zai cika mana nashi alkawarin.
Komai a lissafe yake addini ba aka bane ba, Allah yana cewa idan kuka taimaki addinin Allah sai Allah ya taimaka muku. Allah bai canza wa mutane sai sun nemi su canza wa kawukansu! To, Menene ma'anan chanza wa? Idan mutum ne rago marar sallah dare yanzu ka canza ko mutum mai jin kai amma Yanzu ya canza, to, kunga ire-iren wannan Allah yake so.
Idan kana son samun yardan Allah sai ka Shiga wajen wanda suke son sauyin addini. Mu duniya sanda ne na dogarawa zuwa wajen Allah. Da aka raba malam da komai sai Malam ya daina ? Duk abinda aka sani an raba Malam dasu iyalansa da gidansa da littattafansa sai Malam ya daina addini?.
Idan muna son saiyi da gyara sai mun koma zuwa ga gyara kawukan mu. Shi karatu da gyaran kai tare ake yi saboda haka ko Menene kai ne ma'auni kai zaka fara sai Allah ya cigaba. Allah (T) yana cewa; Yaushe Allah ya musu shiriya? Da nasan 'Dan'uwa duk inda ka Gandhi zaka ga akwai Alkur'ani a cikin aljihunsa, kokuma kaga mutum yana cewa a taya mu da addu'a da can INA tashi sallah dare Karfe 12 ko karfe 1 na dare amma Yanzu sai gashi INA tashi 2 ko 3 dare yanzu haka Matasan mu suke ?.
Almuhim dai shine mu zama masu karatun Alkur'ani, Alhamdulillah yanzu akwai tahafis a cikin 'Yan'uwa wanda ake koyar da yaranmu. Abu na gaba shine 'yan'uwantaka misali ada can mutane da daman gaske in an hadu kuka ake saboda 'yan'uwantakar da Ke tsakanin mu. Malam ya kasance babban abin koyi a wajen mu domin ya salla komai nashi wajen nuna 'yan'uwantaka.
A wani waje wai 'Yan'uwa suna zare wukake a cikin mu wa'iyazubillah. Daman ita Gwamnatin tace sai ta lalata 'ya'yansu su zama suna fada da iyayensu. A cikin jawabin Malam ya kawo musalin wanda ya mari babansa kawai don ya tashe shi yayi Sallah. A cikin jawabin sa ya tabo batun dogo da kai,
Daga Jawabin Sheikh Yakub Yahya Katsina wanda ya gudanar jiya 2/Feb/2020 a garin Bauchi wajen jawabin Rufe Mu'utamar Amm na Dandalin Matasa Harka Islamiyya karo 27.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates
#FreeZakzaky