Ga wani bangare na jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a ranar Alhamis 10/9/2009 dangane da nufi da kuma shirin da gwamnatin Umaru Musa ‘Yar’adua ta yi na ganin bayansa a kwanakin karshen watan Ramadana:
![]() |
SHAIKH IBRAHIM EL ZAKZAKY |
“….To, sai muka samu wani abin da ake ce ma ‘blue print’, rubutaccen bayani kan tsarin da aka yi, (a cikinsa) sai aka ce, tsakanin 16 zuwa 19 ga watan Satumba za a yi ‘operation’. Sai aka fadi ‘blue print’ din ‘operation’ din, cewa za a yi a Zariya ne. Kuma ni ban taba ganin wannan kalma ba, amma wannan na ganta an rubuta a ‘blue print’ din gwamnati; za a yi abin da suka kira ‘massacre’. Kun san ‘massacre? Kisan-kiyashi. Za a shekar da jinane. Wato, suka ce za a kashe kowa ne, da mai zanga-zanga (Muzahara) da dan kallo da mutumin gari. Kuma har suka ce za a tsaya a ‘check-point’, don wai sun yi kuskure a Maiduguri, sun rika harbe mutane a check-point ido na gani, saboda haka wannan karon ba za su yi wannan ba. Za su tsaya a check-point ne sai su kwashe mutanen da suke son kashewa su kai su wani wuri sai su yi abin da za su yi. Sannan kuma (suka ce) duk garuruwan da ke kusa da Zariya, za su bude musu wuta, cewa ainihin Shi’a sun gudu sun je garin. Wanda yake nufin za su bude wuta ta kowane hali kawai akan mutane.
Cikin daren jiya, (9/9/2009) sai muka samu labarin cewa, barikin soja an shirya su a kan batun za a yi wani ‘operation’ a jiyan. To dama akwai wata magana da na ji, cewa su sojoji an musu jawabi an fada musu cewa a goman karshen watan Ramadana ‘yan Shi’a sun ce wai za a yi juyin-mulki. To kuma za a yi kokari a hambare wannan juyin-mulkin. To kaga suna shirya kwakwalen soja da cewa za a aika su su yi kisan kai kenan. To, sai jiya cikin dare labari ya zo mana cewa, lallai an tara soja an fada musu cewa a cikin daren za a yi ‘operation’. Aka ce musu operation din kamu ne, amma idan kamun bai yiwu ba, za a yi mataki na gaba. Amma su masu fada mana labarin sun ce basu san wa za a kama ba, basu san kuma meye mataki na gaba din ba.
Ala-ayyi-halin dai, muna nan muna sa ido. Sai labari can cikin dare ya zo mana daga Abuja, (wannan kuma amintaccen ‘source’ ne), cewa ‘operation din nan a gidan da nake kwana za a yi, kuma abin da suka yi niyyar yi shine za su yi ‘bombing’ din gidan ne. Bombing sosai, za su jefa bam su tarwatsa gidan gaba daya.
(Yadda za a yi operation din shine); Za a aiko da ‘signal’ ne daga Abuja, in an aiko da signal cewa a yi ‘carry-out operation’ din, akwai wadansu (jami’an tsaro) da za su taso daga Kaduna sai su iso su hadu da na Zariya sai a wuce, wannan aikin na tarwatsa gidana da bom.
To, dama har akwai masu ce min, to ko daidai wannann lokacin zai zama bana gidan ne? Nace Allah ya sauwake. Gidan da ake so a tarwatsa, ina amfanin na rayu bayan an tarwatsa iyalina? To, amma muna da labarin cewa sun ce za su gama da al’amarin Zakzaky zuwa gobe Juma’a ne. Za su gama. Mai yuwuwa tunda ba su yi jiya ba, ko yau da daddare za su zo.
Har ma, muna da labari a nan unguwar da nake zaune da ake ce ma Gyallesu, akwai wasu mutane daidaiku, duk cikansu ‘yan kungiya ne, lallai sun bar unguwar. Kuma an ji ta bakinsu cewa, za a yi kisan kiyashi ne, saboda haka ko kusa da unguwar kar wani ya je, tunda za a yi kisa, saboda haka sai bayan an gama kisan za su dawo.
Ku masu yunkurin kisa, in dai kisa ne an kashe mutane wadanda suka fi ni. Saboda haka ba abin mamaki bane a kashe ni. Amma ina ganin babu bukatar ku saka Bom ku tarwatsa gidan da nake kwana. Domin a gidan nan akwai mahaifiyata ‘yar shekaru 88, kuma bata muku komai ba. Akwai kuma yara kanana, wadanda su ma basu muku komai ba. Ni kasheni ba wani abu bane, kuna iya kashewa, an kashe wanda suka fi ni a wannan zamanin da da, saboda haka in ma an kashe ni sunnah ne. Amma mene ne naku na kiyayya da za ku yi wannan?
Musamman kai Umaru Musa ‘Yar’adua, wanda suka sa ka, suka ce wai kai ne shugaban kasar nan, kuma kake tunanin cewa za ka burge su. Yanzu za ka burge Amurka da Isra’ila idan ka kashe AlZakzaky. Sun daura ka a kan cewa yanzu za ka yi kisan kai, kila don ka samu fuska kila a wajensu. To, sunna za ta maimaita kanta. Ni, na yi burin ace wanda zai kashe ni, ya zama wani mutum wanda bashi da rabon Lahira ne, amma ni ka ban mamaki saboda ina jin tausayinka, kamar yadda nake jin tausayin yayanka da aka kashe. To, amma in haka ka so, shikenan, falillahil-ham! Amma dai rokona shine ka kashe ni ni kadai, ba bukatar ka yi ‘massacre’, ba bukatar yin kisan-kiyashi. Ba bukatar kashe mahaifiya da ‘ya’yana, sukai maka mene? Da kuma makwafta ma. Duk sukai muku mene?
Ku kuma wadanda za ku yi kisa kar ku dauka za ku samu wani matsayi ne. Ita da’awa ba za ta mutu ba. Don an kashe ni ba yana nufin shikenan da’awa ta mutu ba. Insha Allahu sai dai ta yi karfi, domin ainihin da’awa Alhamdulullahi, ta riga ta shiga zukatan mutane, kuma lallai bindiga ba zai bindigeta ba. Ko da kuwa kun yi abin da kuke cewa za ku yi wai shi kisan-kiyashi, ‘massacre’!
Ga wadanda ake kira Malamai; Hukumar da take cewa ba ruwanta da addini, ko dutse kana iya bautama ko itace. Furuci suke yi sosai, muraratan, ko dutse ko itace kana iya bautama, to sune kuma za su kashe muku wadansu ma’abota addinin da ba ku so, sai su barku ku ku yi addini? Ma’ana su za su muku jihadi addininku ya tabbata? Haka kuke tsammani. Sai muce muku, to wannan abin da kuke tunani mafarki ne. Ba zai yiwu ya zamana wai nizamin da ba ruwanshi da Allah, ba ruwanshi da addini shine zai tabbatar muku da addini, ya maishe ku Malamai ba.
Al’ummar Musulmi kuma don su gane, (su al’umma suna iya ganewa); In kaji wani mutum yana da’awa, yana cewa a kashe Musulmi, sawa’un Musulmin nan ko mene ne ra’ayinsa, ko yace masa dan tatsine ne, ko yace masa dan kala-kato, ko yace masa dan Boko Haram, ko yace masa dan Darika, ko yace masa Dan Shi’a, ko yace masa dan mene ne, in dai yace a kashe Musulmi ne mai shaidawa da La’ilaha illalah, Muhammadur Rasulullah, to wallahi summa tallahi, Yahudawa yake ma aiki. Kuma makiyinka ne kai, in ka yi Imani da La’ilaha illalah, Muhammadur Rasulallah, ko meye ra’ayinka.
Mutum ko meye ra’ayinsa a addini akalla dai Musulmi ne, to yaushe kai za ka nemo wanda ba ruwansa da addini, bai san addini ba, shine zai maka jihadi addininka ya kafu? Ballantana in dai Musulunci ne kake yi da gaske, to ya kamata ka ji tausayin wanda kake ganin bai gane gaskiya bane, in kai kana kan gaskiyar ne. Ka kira shi da tausayi domin ya gane. Don shine sunnar na farko.
Amma ba zan karkare maganar nan ba sai na yi muku albishir, cewa ko an ki ko an so addinin Allah zai tabbata. Ba yadda za a ce bakin bindiga ko Bom ya tarwatsa da’awa ya zuwa ga Allah, saboda da’awar nan bata doru a kana a kashe wani ba, ko ana barazana ga rayuwar wani ba, ta doru akan hankali ne da ilimi da kuma hujja, shine kuma mutane suke ji su gamsu.
Ni dai kam Alhamdulillahi, gaskiyar magana ita ce, ni abin alfahari ne ya zama an kashe ni a kana bin da nake yi. Abin alfahari na ne. Dama ko ba a kashe ni ba, yau shekaru 30 kana ta da’awa, abu daya, kuma ana ta yunkurin a kashe ka sam baka kasu ba, kuma har da’awa ta kafu daram, ba yadda za a yi da ita. Komai tsiyan mutum dole sai da’awar nan ta habaka ta tabbata. Kuma bamu tsammanin za ta tabbata muna nan ne, amma dai za dai ta tabbata din. Saboda haka idan wannan ne (yunkurin kashe ni) ya zama ya muku, sai muce to, shikenan. Kar ku dauka mu za mu yi ko gezau! In ma yau da daddare ne kuke so ku zo, ko ma wani dare ne, to ina nan a gida. Amma dai kamar yadda nake rokonku, in kun ji rokon shine, ba bukatar ku kashe mahaifiyata da ‘ya’yana da iyalina. Ni kawai ku zo shikenan, duk yadda kuke bukata sai ku yi abin da za ku yi. Insha Allah.”
Tags:
Daga marubata