Tsarabar Katama Na Mu'utamar Ɗin Dandalin Matasa A Bauchi!!! Rubutu Na Biyu (2)


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DANGANE DA RASHIN TSARO 

Cigaba:-

Da yake magana kan rashin tsaro a qasa wanda ya samarwa al'umma rashin aminci, ya nuna cewa ;

Shi aminci na samuwa ne ga wadanda su kayi imani, domin komai firgici su suna cikin aminci. Amma wani zai iya cewa, to, ai mu 'yan gwagwarmaya ne, amma me yasa muke cikin tsoro? Sai malamin ya bada amsa da cewa;

To, ai shi aminci ana samunsa ne bayan tsoro.

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ZA MU CANZA MUSU DA AMINCI BAYAN TSORO .‘’

‘’ DUK WANDA YAYI IMANI DA ALLAH ZAI SHIRYAR DA ZUCIYARSA (ya sami aminci ).‘’

Sannan kuma , ‘’ DUK WANDA YA JIBINCI ALLAH DA MANZONSA DA KUMA WADANDA SU KAYI IMANI, LALLE RUNDUNAR ALLAH ITA CE MAI RINJAYE .‘’

Ya cigaba da cewa, idan kaga kana ta yi amma ba kaga canji ba, to, wala-Allah matsalar daga gare ka ce. Ma'ana ka binciki wilayarka, sadaukarwarka da sallamawarka. 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ A YAYIN DA SUKA BAQANTA MANA (rai )SAI MUKA KAMA SU DA ZUNUBANSU....‘’

Saboda haka ba mun zo duniya don mu zauna bane, ita duniya sanda ce ta dogarawa zuwa ga Allah . 

Dole mu kasance masu tawakkali , domin su Manzanni (A.S ) ma an umarce da suyi, to, ina kuma ga mu? Amma dai kaine ma'auni , wanda yayi mai kyau kansa, wanda ma ya saba domin kansa .

NEMAM LAHIRA BA CHATING BANE

Malamin ya nesantar da neman lahira da cewa ba chating bane;

‘’ ITA NEMAN LAHIRA BA CHATING BANE, DUK MAI SON LAHIRA TO DOLE YAYI FADI-TASHI  WAJEN NEMANTA .‘’

Malamai bai qarqare jawabinsa ba har sai da ya nuna takaicinsa game da yadda 'yan'uwa suka kasance a yanzu na cin naman junansu.

Yace, ada 'yar'uwa na qaunar junansu fiye da yanzu, ta yadda za kaga dan'uwa na qaunar dan'uwansa na harka fiye da 'yan'uwantaka ta jini, har ma za ka ji jama'ar gari na fadin haka. Amma yanzu sai ka samu 'yan'uwa na zama suna cin naman 'yan'uwansu.

Wannan kuwa na daya (1)daga cikin ribar da maqiya suka ci, domin sunce sai sun samar da yanayin da zai raba tsakanin 'yan'uwa ta hanyar shiga tsakanin iyaye da 'ya'yayensu.

WANNAN TAQAITACCEN JAWABI DANA KAWO BA LALLE A JI SHI KAMAR YADDA AKA YI RECORDING BA. NA 'DAN TSATTSAKURO NE (jotting )DAGA ABINDA NA JI DON AMFANAR DA WADANDA BA SU SAMI HALARTA BA.


ALLAH YASA MU AMFANA DAGA JAWABAN ALMAJIRAN SAYYID (H )NA HAQIQA.

👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        08137925034

~2nd February , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post