REAL MADRID |MUNA DA MATSALAR CIN KWALLAYE DA YAWA

INJI MAI HORAR DA KINGIYAR

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real
Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa kungiyarsa tana
shan wahala wajen zura kwallaye a raga a saboda hakane
yace dole zai zauna domin shawo kan matsalar.


Dan wasa Karim Benzema ne ya yanke hukuncin yadda
wasan hamayya na birnin Madrid ya kasance da kwallonsa ta
farko da ya tava cin Atletico a filin wasa na Santiago
Bernabeu tun farkon zuwansa Real Madrid.

Dan wasan kasar Faransan ya zura kwallon ne a minti na 56
daga kwallon da dan wasa  Ferland Mendy ya ba shi bayan
Vinicius Jr ya sarrafa kwallon a bangaren hagu inda kuma
nan take ya kaita cikin raga.

Atletico Madrid wadda ke matsayi na biyar, ba ta ci wasa ba
a cikin biyar da ta buga kuma ba ta buga kwallon kirki ba a
yau, duk da cewa Angel Correa ya buga kwallon da ta daki
tirke kuma itace babbar danar da ukngiyar ta samu.

Real Madrid za ta iya cin sama da haka da a ce ,ai tsaron
raga Jan Oblak bai kare damarmaki guda biyu da Vinicius ya
buga ba kuma shima dan wasa Fede Valverde yay buga wata
kwallo sai dai ta tashi sama.

Wasa na 21 kenan da Real Madrid ta buga ke nan ba tare da
an doke tawagar Zinedine Zidane din ba kuma ta ci takwas a
jere, ciki har da bugun finareti da suka yi da Atletico din a
wasan karshe na Spanish Super Cup.

Bayan tashi daga wasan ne Zidane ya ce akwai bukatar ‘yan
wasansa na gaba su tashi tsaye domin cigaba da zura kwallo
a raga saboda a ‘yan kwanakin nan basa samun damar zura
kwallaye a raga yadda ya kamata.

 ME ZAKU IYA CEWA AKAN WANNAN MAGANAN KUCI GABA DA KASANCEWA DA WANNAN KAFA TAMU DOMIN SAMUN LABARAI 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post