Minene Fibers, Kuma Wane Amfani Suke Yi A Jikin Ɗan Adam???



                     Chuta da magani

Daga: M.N.N Updates

Tareda: Jibril Usman Sarki (08149953832)

Su _fibers_ kmr tsintsiya suke a ciki. Suna taka rawar gani matuka dan gane da lafiyar mutum. Wannnan sinadarin na *fibers* anfi samunsa wajen 'ya'yan itatuwa daban daban da muke mu amala dasu.

Cikin dan adam kusan shine bola a jikin sa,kome ka d'ebo shi zaka zubawa me kyau da marar kyau,me cuta da marar cuta. Sbd hka dole se ana kula dashi. Abubuwan da ke gyara shi kuwa an hadasu a cikin abincin mu wasu da muke ci daga ciki musamman fruits.

*Wani sa in zaka wayi gari  ka yini baka samu tsugunni ba, wnda muke kira ( *constipation* ) har kila ma kai kwanaki akalla uku ko hudu. Sbd hka zka takuru matuka, to anan aikin fibers ne su share cikin su fitar da duk wni datti daya kawo mtslr.

*Ga masu basir,sukan samu zafi wajen ba haya kaji kmr ana yayyanka maka dubura,kaita nishi,kana dafe ciki. To anan ma aikin *fibers* ne da ansha yayan itatuwa masu sinadarin *fibers* zaa warke.

*Haka kurum wataran zakaci wani abun ya daure maka ciki,kaje ba haya kaji yafi ma ace haihuw zakai dan yafi sauki,har ma kaji ko wni abu zaka saka ka janyo shi dan ka samu afuwa,kaji kana ta faman nishi da zufa ka rasa inda zaka saka kanka,da kyar ka samu kayi ka tashi,to wannann ma aikin *fibers* ne. Da ansha dan itaciya me wannan sinadaran zaa warke.

*Wasu kuma sunason rinka ba haya akai akai kmr kowa,ko kuma sun lura yaransu basa ba haya _normal_ sbd hka shan yayan itatuwa masu wannan sinadarin zai gyara damuwar.
  To se dai in kana da wannn Matsalolin baa son kasha wani magani da zai sa bayarka ta kara tauri ana son ire iren maganin ka kaura ce masu. Misali  *metronidazole* tab ko syrp ( wato flagin) cps *tetracycline* 500mg ( ja da yalow) *loprimide* cps ( anti diarrhea ) dss. Su wadannan magun gunan zasu saka baho na bahaya na ciki ya daure bahaya taki fita.
  Sannan idan normal kake bahayrka bata da wata mtsl to kada ka rinka yawan mu amala dasu musamman wasu daga ciki sbd zaka rinka yawan zugunno kuma kaga takura ta shigo.

Waddan nan 'yayan itatuwa masu dauke da *fibers* nada yawa amman zan lissafo masu saukin samu kuma wnda muke sha yau da kullum. misalinsu

1. Kan kana

2. Abarba ( *pineapple* )

3. Ayaba ( *Banana* )

4. Gwanda ( *pawpaw* )

5. Mangoro ( *mango* )

6. Lemun zaqi ( *Orange* )

Da fatan za'a rinka jarabasu. In anga baa samu saukiba  se a ziyarci asbt.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post