Sheikh Zakzaky (H) Da Haramtacciyar Shari'a A Kotun Kaduna!!!



Ma'asumah Nigerian News Update,
 Tare da Comrade Naziru Saidu Gusau

".. Mu aka kawo mana hari, Aka bude mana wuta, Aka harbemu da bindiga, Aka kashe mutane sama da dubu ciki harda Ya'yanmu,

Ni da mata ta, an harbe mu, aka jamu, Ni anja ni akan gawan Ya'yana ne, Sannan kuma aka kawo mu nan aka kulle duk cikarmu da harsasai a jikinmu, Yanzu haka muna fama da ciwo, Yanzu duk jikinmu nan muna da harsasai,

To Sannan, mu muka kai kara kotu, Mukace don me ake tsare damu? Suka tura Lauyan gwamnati, Yace suna tsare damu ne domin su kare mu,

Kotu bayan ta gama Jin kowanne, ta fitar da hukumci cewa, lallai ba wata doka a Nigeria da wanda Nigeria ta samawa hannu na kasar waje, wanda ta ba da dama gwamnati ta tsare wani mutum da sunan tana kare shi,

Saboda haka sai (Kotu) tayi hukumcin cewa a sake mu ba tare da gindiya sharadi ba,

Yau an kwashe kusan shekara da watanni shiru basu bi umarnin wannan kotun ba,

 *SANNAN KUMA YANZU KAZO (BUHARI) KACE KA KAWO ZA'A KAI NI KARA?* "

- Shaikh Zakzaky (H).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post