Tsarabar Katama Na Mu'utamar Ɗin Dandalin Matasa A Garin Bauchi!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YA NUNA TAWARI'U CIKIN GABATAR DA KANSA.

Shugaban dandalin matasa na qasa ne ya gabatar da babban baqo Sheikh Ya'aqub Yahaya  Katsina ta hanyar yaba kyawawan tarbiyyar da ya samu daga su Sayyid ( H )da kuma jajircewar sa kan wannan harka.

Bai kai ga inda zai tsaya ba cikin hanzari  Sheikh ya karbe abin maganar daga hannunsa yace;

‘’ DA NA SAN IRIN WADANNAN KALAMAI ZA KA FADA LALLE DA NI NA GABATAR DA KAINA BA KAI BA.  NI NE YA'AQUB YAHAYA KATSINA ALMAJIRIN SAYYID (H ).‘’

Daga nan ya cigaba cikin jawabinsa me ratsa zukatan bayin Allah salihai.

Dangane da halin da wannan al'umma ke ciki ya nuna cewa lalle yanzu fada da Allah ake yi ba batun yin nisa ga Allah ba. Domin yin nisa ga Allah yana nuna nisantarsa ne ta hanyar bijere masa, yaqarsa kuma shine yin fada da abinda yayi umarnin a aikata shi.

Ya nuna cewa hadafin Sayyid (H )shine yaga al'umma ta dawo hanyar Allah ba wai ya wai kafa Gwamnati ba. Domin tabbatar addinin Allah lissafi ne, ba zai taba canzawa ba.

‘’ SUNNAR ALLAH CE WACCE TA RIGA TA GABATA, BS ZA KA TABA SAMUN CANJI BA......‘’

Kuma dole ya kasance a tashi ayi aiki kafin samun yardar Allah. Aiki ne zai sa a sami yabo kamar yadda Manzon Allah(S.A.W.W ) ya yabi wasu daga cikin sahabbansa irin su Abu Zarr Al-Gifari cewa;

‘’ ALLAH BAI YI WANI HARSHE MAI FADAR GASKIYA KAMAR NA ABU ZARR BA.‘’

Ya kuma ce;

‘’ SALMANU NA DAGA CIKINMU AHLUK-BAIT .‘’ 

Su Imam Ali (A.S )kuwa 'yan cikin gida ne ba sao ance wani abu a kansu ba.

Shehin malamin ya kawa ayar da Allah (T )ke cewa;

‘’ YA KASANCE HAQQI A KANMU TAIMAKON MUMINAI .‘’

Yace, sai dai wannan taimako yana faruwa ne cikin wadanda suka cancanci hakan. Sannan kuma  Allah ba zai taba sallada kafirai akan muminai ba.

Sai dai kuma malamin ya yi tambaya cewa,

To, ya akayi kuma Allah ya sallada kafirai a kanmu?Tambaya ce da kowa ya kamata ya tambayi . Shin , Allah (T )me canza maganarsa ce ? Lalle ayyukanmu da rashin yin abinda ya kamata ne yasa hakan, amma Allah bai kasance yana canzawa ba. Duk abinda kaga ya canzu, to, daga mutane ne.

‘’ LALLE ALLAH BA YA CANZA ABINDA KE GA JAMA'A HAR SAI SUN CANZA ABINDA KE GARE SU.‘’

Lalacewarmu ce za tasa kafirai su sami sulda a kanmu.

ZA MUCIGABA INSHA ALLAH.

Daga wakilanmu na  Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

~2nd February , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post