Abu Mafi Wuya Shine Samun Wadda Zata Iya Zama Dakai Da Hakinka!!!


🇮🇪Ma'asumah Nigerian Newa Update

Daga wakilinmu
MJ Matashi Ibrahim

Maryam Sanda: Kafin kayi aure, ka bari budurwarka ta kama ka sau biyu kana cin amanarta – Shawarar wani ga samarin Najeriya

Wani saurayi ya shawarci samari akan yadda za su gwada hankalin ‘yan matansu kafin su auresu, ya bayyana cewa hanya daya ce, ita ce saurayi ya bari budurwarshi ta kama shi yana cin amanarta sau biyu ko sau uku kafin ya aureta.

Ya ce yin hakan shine zai bawa mutum kwanciyar hankalin cewa matar tashi ba za ta kashe shi ba koda wani abu makamancin haka ya faru bayan aurensu.

Mutumin mai suna Chidi Ogudu ya bayyana haka ne a yayin da yake sharhi akan hukuncin kisa da aka yankewa Maryam Sanda, wacce aka kama da laifin kashe mijinta, bayan ta gano cewa yana cin amanarta.

Ya ce yana da matukar muhimmanci maza su gwada yin hakan, kuma su tabbata ‘yan matansu sun kama su suna cin amanarsu kafin suje ga aurensu. Idan har ba ta dauki wani mataki a wannan lokacin ba to shikenan mutum zai iya aurenta, amma idan ta dauki wani mataki sai ya canja wata.

Saurayin ya bayar da misali da tsohon fitaccen mawakin nan na Najeriya, Tuface, onda yace yanzu kome Tuface zai yi matarshi Annie babu abinda za ta yi masa saboda ta riga ta san halinshi tun kafin suyi aure.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post