Sanders Ya Ce Idan Ya Ci Zabe Zai Sake Yin Nazari Kan Mayar Da Ofishin jakadancin Amurka Birnin Quds

Dan takarar shugabancin kasar Amurka a jam’iyyar Democrat Bernie Sarders ya bayyana cewa, zai sake yin nazari kan dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Quds da Trump ya yi.
(ABNA24.com) Dan takarar shugabancin kasar Amurka a jam’iyyar Democrat Bernie Sarders ya bayyana cewa, zai sake yin nazari kan dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Quds da Trump ya yi.

Sanders ya bayyana haka ne ne a muhawarar da ‘yan takarar neman shugabancin kasar Amurka a karkashin inuwar jam’iyyar Democrat suka yi ne a jihar Nivada, inda ya bayyana cewa, matakin na Trump na son rai ne kawai.

Ya ce yana alfahari da cewa shi bayahude ne a akida da addini, amma kuma bai yarda da tsatsauran ra’ayi irin na Netanyahu ba.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, akwai bukatar a sake yin nazari kan siyasar Amurka a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa duk da cewa tsaron Isra’ila yana da muhimmanci ga Amurka, amma bai kamata a manta da matsanancin halin da aka jefa al’ummar Palastinu ba.

Yanzu haka dai Sanders shi ne kan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasar Amurka a karkahsin inuwar jam’iyyar democrat, wanda kuma ake ganin idan ya tsallake zaben fitar da gwani, zai iya zama wanda zai kara da Trump a zaben shugaban kasa.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post