Shugaban majalisar juyin juya hali a kasar Yemen ya bayyana hadin kan al'ummar kasar Yemen wajen tunkarar makiyan kasar da cewa babban sako ne gare su.
(ABNA24.com) A cikin wani rahoton da tashar talabijin din alalam da ta bayar, ta ambata cewa Muhammad Ali Alhuthi shugaban majalisar juyin juya hali a kasar Yemen, ya bayyana cewa; tsayin daka da al'ummar kasar Yemen suka yi tare da hada kai wajen tunkarar masu mummunan kudiri kan kasar, sako ne mai matukar muhimmanci ga dukkanin al'ummomin duniya.
Haka nan kuma ya ce tun shekaru biyar da suka gabata, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa tare da taimakon Amurka da Birtaniya, suke kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da ta ruwa, tare da killace kasar Yemen baki daya, tare da hana shigo da abinci da magunguna da makamashi a cikin kasar, bayan kisan dubban fararen hula mata da kananan yara, amma duk da haka al'ummar Yemen ba su mika kai ga manufofin 'yan mulkin mallaka da 'yan korensu na yankin ba.
Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa, a cikin wadannan shekaru biyar, al'ummar kasar sun kara samun gogewa a bangarori daban-daban na kariyar kai, da hakan ya hada da inganta makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marassa matuki, wadanda da su ne suke kare kansu, ta hanyar mayar da martani kan makiyan al'ummar kasar, wanda kuma hakan zai ci gaba matukar dai masu kaiwa kasar hari tare da killace ta ba su dakatar da yin hakan ba.

Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Tags:
Labaran Duniya