Nigeria: “Yan Ta’adda Sun Kai Wa Karamar Hukumar Chibok A Jahar Borno Hari

Kungiyar ‘yan ta’adda ta; Daular Musulunci A Yammacin Afirka” ( ISWAP) ta kai hari a garin Bambula da ke karamar hukumar Chibok a jahar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
(ABNA24.com) Kungiyar ‘yan ta’adda ta; Daular Musulunci A Yammacin Afirka” ( ISWAP) ta kai hari a garin Bambula da ke karamar hukumar Chibok a jahar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Da jiffifin safiyar jiya Laraba ne dai ‘yan ta’addar su ka kutsa garin na Bambula inda su ka yi awon gaba da Muhammad Abba wanda shi ne kwamandan rundunar sa-kai ta Cvilian JTF tare da wasu mutanen.

Wannan harin dai ya zo ne kwanaki kadan bayan wani kwatankwacinsa da ‘yan ta’addar su ka kai a garin Kwallangulum a cikin karamar hukumar ta Chibok, inda su ka kona gidaje.

Wani mazaunin garin ya fadawa kafafen watsa labaru cewa; Maharan sun fito ne daga dajin Ajigum Talata da can ne babban sansanin ISWAP, sannan su ka yi wa gidan Abba tsinke tare da yin awon gaba da shi.”

Sunan garin Chibok ya fito fili ne dai a 2014 da ‘yan ta’addar Boko Haram su ka sace dalibai mata fiye da 200 daga wata makarantar kwana.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post