Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya baiwa ma’aikatar kiwan lafiya ta kasar umurnin kafa wani kwamiti na musamman domin tunkarar barazanar cutar nan mai shafar numfashi ta coronavirus a kasar da nufin murkushe ta.
Rohoton (ABNA24.com) Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya baiwa ma’aikatar kiwan lafiya ta kasar umurnin kafa wani kwamiti na musamman domin tunkarar barazanar cutar nan mai shafar numfashi ta coronavirus a kasar da nufin murkushe ta.
Kwamitin wanda na hadin guiwa ma’aikatun kasar da dama ne zai kasance na karkashin sanya idon gwamnati.
Manyan ma’aikatun da kwamitin ya kunsa, sun hada da ma’aikatar cikin gida, da ta sufiri da ci gaban birane, da ilimi da kimoya da bincike da kuma fasaha, da al’adu da yawan bude ido da addini da bangaren soji da kuma hukumar kula da gidajen radio da talabijin na kasar da kuma hukumar kula da tsara aikin hajji da umara.
Kasashen da aka samu mutanen farko farko da suka kamu da cutar a baya baya nan sun hada da Afganistan, Bahrein, Koweit da kuma Iraki.
Hukumar WHO, ta bayyana a yau Litini cewa dole ne kasashen duniya su tashi tsaye domin fuskantar barazanar annobar ta Covid-19.
Kawo yanzu dai mutane sama da 2,600 ne cutar ta kashe a kasar China tun bayan bullarta a watan Disamban bara.
Kwamitin wanda na hadin guiwa ma’aikatun kasar da dama ne zai kasance na karkashin sanya idon gwamnati.
Manyan ma’aikatun da kwamitin ya kunsa, sun hada da ma’aikatar cikin gida, da ta sufiri da ci gaban birane, da ilimi da kimoya da bincike da kuma fasaha, da al’adu da yawan bude ido da addini da bangaren soji da kuma hukumar kula da gidajen radio da talabijin na kasar da kuma hukumar kula da tsara aikin hajji da umara.
Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Iran dai na daga cikin kasashen da cutar mai shafar numfashi ta coronavirus da ake wa lakabi da Covid-19 ta bulla a baya baya nan inda kawo yanzu ta kashe mutum 12.Kasashen da aka samu mutanen farko farko da suka kamu da cutar a baya baya nan sun hada da Afganistan, Bahrein, Koweit da kuma Iraki.
Hukumar WHO, ta bayyana a yau Litini cewa dole ne kasashen duniya su tashi tsaye domin fuskantar barazanar annobar ta Covid-19.
Kawo yanzu dai mutane sama da 2,600 ne cutar ta kashe a kasar China tun bayan bullarta a watan Disamban bara.
Tags:
Labaran Duniya