A Jamhuriyar Kamaru, daruruwan ‘yan kasar ne suka gudanar da wata zanga zanga ta yin tir da tsoma bakin shugaban kasar Faransa a harkokin cikin gidan kasar ta Kamaru.
RAHOTON ABNAHAUSA.COM (maasumah.com.ng) A Jamhuriyar Kamaru, daruruwan ‘yan kasar ne suka gudanar da wata zanga zanga ta yin tir da tsoma bakin shugaban kasar Faransa a harkokin cikin gidan kasar ta Kamaru.
Masu zanga zangar na bukatar shugaban kasar ta Faransa Emanuel Macron ya shiga tafiye tafiyensa, don kuwa kasar ta Kamaru ba yanki ne ba dake karkashin ikon Faransa, kasa mai cin gashin kanta dake da ‘yanci tun a cikin shekara 1960.
Dangantaka tsakanin Kamaru da kuma kasar ta Faransa ta yi tsami ne a farkon makon da ya gabata, bayan da shugaba Macron ya bayyana cewa zai yi matsin lamba ga gwamnatin kasar ta Kamaru kan yadda ta ke tafiyar da siyasar ta ta cikin gida.
Batun da gwamnatin Kamarun ta bayyana cewa matsalar data shafi Kamaru, matsala ce data shafi ‘yan kasar, wadanda kuma su ne ke da nauyin samar wa kansu mafita.

Tags:
Labaran Duniya