Pentagon: Adadin Sojojin Amurka Da Su Ka Jikkata Sanadiyyar Harin Iran A Iraki Ya Karu Zuwa 110

Ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne a jiya Juma’a wacce ta tabbatar da cewa sojojin 110 sun sami raunuka a kwakwalensu. 

Wannan ce sanarwa ta karshe wacce ta ke nuni da karuwar yawan sojojin na Amurka da makamai masu linzami da Iran ta harba akan sansanin sojan Aynul Asad da ya ke kunshe da sojojin Amurka a kasar Iraki.


Sanarwar ta ci gaba da cewa; sojoji 77 sun sami magani sun kuma warke sannan sun koma bakin aiki. Har ila yau, an kai wasu sojojin 35 zuwa asibiti a kasar Jamus. Sai kuma wasu sojojin 25 da aka kai su kasar Amurka domin samun magani.

Tun bayan da Iran ta kai harin daukar fansar kisan shahid Kassim Sulaimani, akan sansanin sojan Amurka da ke kasar Iraki, a ranar bakwai ga watan Janairu shugaban kasar Amurkan Donald Trump ya kore cewa da akwai wanda su ka jikkata.

Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post