Pompeo: Akwai Sabon Shiri Na Tunkarar Kutsen Kasar Iran A Yankin Asia Ta Kudu

Pompeo: Akwai Sabon Shiri Na Tunkarar Kutsen Kasar Iran A Yankin Asia Ta Kudu


Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana wasu akwai sabbin shirye-shiyen gwamnatin kasar na fuskantar kasar Iran, wadanda su ne sabbin takunkuman tattalin arziki, wadanda yake ganin zasu yi wa kasar doka na karshe.
(ABNA24.com) Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana wasu akwai sabbin shirye-shiyen gwamnatin kasar na fuskantar kasar Iran, wadanda su ne sabbin takunkuman tattalin arziki, wadanda yake ganin zasu yi wa kasar doka na karshe.

A hirar da ta hada shi da wata mujallar kasar Amurka mai suna “The Washington Free Beacon” Pompeo ya ce Amurka zata maida dukkan takunkuman da aka dorawa kasar Iran a can baya, wanda a fadinsa zai kawo karshen yarjejeniyar Nukliya ta 2015 kwata-kwata.

Pompeo ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zawa ne zai bukaci kwamitin tsaro na MDD ya maida dukkan dakunkuman majalisar wacce aka dorawa kasar ta Iran kafin yerjejeniyar shekara ta 2015.

Sai dai a nan ma sakatarin harkokin wajen na Amurka ya nuna shakkunsa kan samun goyon bayan kasashen turai a wannan bangare.

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post