MUHIMMAN CIN HIJABI GAREMU MATA
Abbagano✍
(part 1)
Hijabi alama ce ta kunya,ita Kuma kunya Tana daga cikin kyawawan dibi'u,Wanda musulunci yake Kira zuwa garesu, kunya Tana daga cikin runduna, cikin rindunonin imani,
Sannan kunya nadaga cikin dabi'a Mai kyau cikin dabi'un da musulunci yayi Kira garesu, domin kalmar kunya an tsagota ne daga kalmar rayuwa, tayadda rayuwa Bata tsayuwa saida kyawawan dabi'u.
Menene HIJABI??
Kalmar hijabi a yaran larabci Tana nufin abinda ya lullube abu,
Amman cikin isdilahi na malaman shari'a Kuma, shine:- abinda mace musulma take rufe jikin ta da adonta ga barin ganin duk Wanda ba maharramin ta ba,
Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Allah (t) yayi nuni da wajibcin say cikin littafi Mai tsarki alqur'an( يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا )
الأحزاب (59) Al-Ahzaab
Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.
MUHIMMAN CIN HIJABI GAREMU MATA
Abbagano ✍️
(part 2)
Allah (t) ya wajabta mana saka hijabi,sannan yasanya yazama babbab zunubi ga wacce Bata Sanya ba, saboda haka hijabi yazama Abu Mai muhimman ci da fa'ido ji dayawa Wanda suke komawa gare mu mu mata, sannan fa'idar hakan yana komawa ga mujtama'a namu na 'aluma.
1️⃣ Hijabi yana taimakawa wajan gyara rayuwar matasa, ta hanyar Hana su afkawa zuwa ga aikata alfasha,
Da'ace mata zamu na yin fita Babu hijabi, hakan zaisa matasa suna afkawa cikin matsala.
2️⃣ Hijabi yana sawa mu koma zuwa ga dabi'u masu kyau da nutsuwa cikin dukkan nin motsin mu na rayuwa,
Idan da'ace zamu bar saka hijabi da kullum mun dinga samun afkawa daga mutanen banza.
3️⃣ Hijabi yana Sanya mu mukasan ci allah (t) domin mun aikata umarnin sa dayayi akan mu, Wanda aikata hakan zaisa musami matsayi babba gurin Allah (t).
4️⃣ Hijabi yana sanya mu musami karfin gwiwar aikata sauran aiyuka musulunci, irin su (sallah) (azumi) da sauransu.
5️⃣ Hijabi yana sanya mu boye gashin mu, tayadda maza Jen mu zasu ganmu cikin kyawun mu,sabanin irin yadda yake ganin matan banza Babu hijabi a waje.
6️⃣ Hijabi yana karemu daga cutuwar masu cutarwa, abisa hakane ma Allah yagaya Mana cewa
ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا )
Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.