@Ma'asuma Nigeria News Updates.
A yau Alhamis 27/2/2020 ne, da misalin karfe 12:20pm. Taron ya fara gudana a harabar Makarantar dake a garin Rijau. Ina an fara da bude taro da Addu'a. Sai aka gayyato daya daga cikin dalibai masu sauka Alaramma Abdulwaha Abdullahi ya gabatar da karatun Al-Qur'ani mai girma.
Daga nan ne fa a tsunduma cikin program. Sannan ne aka gayyaci daya daga cikin mawakan Sayyida Fatima na garin ya kamsasa wurin da baitocin yabon yar Manzon Rahma. Sai wakilin yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na garin ya gabatar da jawabin maraba da baki.
Sannan ne aka aka gabatar da daya daga cikin Malaman da aka gayyato , Malam Liman Bakari. Sannan aka gabatar da dalibai masu Sauka su goma sha daya(11).
Bayan da suka gama karatukkan su. Sai babban bako mai jawabi a wurin Sheikh Muhammad Sani Abdullahi Zuru. Inda Shehin Malamin ya fara da godiya ga Allah (S.W.A). Da kuma godiya ga Manzo sa da yazo mana da Al-Qur'anin mai girma. Daga nan ne fa Malam ya shiga bayar da bayanai na hikima da hankali. Inda a cikin jawabin Malamin yake nuna cewa " Manzo rahma ne ya fara kafa makaranta. Inda ya ya karantar da Sahabbansa har zuwa jami'a. Wanda wannan suna na jami'a ya samo asali ne daga Masallacin Juma'an da Manzon Allah yake koyar da sahabban sa." Inda ya kara da nuna cewa "Manzon Allah ne ya fara koyar da sahabban sa waddan nan ilimukkan na zamani, wadanda sun samo a sali daga cikin Al-Qur'ani ne mai tsarki. Inda malam ya bayyana cewa Manzo Allah ya koyar da Mathematic, Physics,Chemistry, harda Biology da sauran su"
Haka dai malamin ya cigaba da jawabin sa, har ya kammala. Inda daga karshen jawabin sa ya nuna cewa "wannan al'amarin na maganar haramta karatun almajiranci. Da nuni da cewa lallai mutane su farka domin wadannan azzalamun ba sa so muyi addini, ko karatun Al-Qur'ani mai girma".
Sannan ne aka gabatar da raba kyautukka. Ga Dalibai bamu sauka su goma 11. Sannan aka mayar da abin magana zuwa ga shehin Malamim domin ya gabatar da Addu'ar rufe taro.
Daga wakilinmu:
Auwal M Tukur
27/2/2020
Tags:
Hotuna