@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TA SHA BAMBAN DA HAIHUWAR DUK WANI BIL-ADAMA
Kamar yadda muka kawo cikin rubutunmu na bay, an haifi Imam Ali (A.S )ne ranat juma'ah, 13 ga Rajab a shekara ta 30 bayan shekarar Giwa, wato shekara 23 kafin aiko Annabi (S.A.W.W )a matsayin dan saqo.
An haife shi (A.S )a cikin dakin Ka'aba, kuma ya fado,qasa yana mai yin sujadah ga Allah mai ajiye baiwarsa inda yaso.
YADDA HAIHUWAR TA KASANCE
Bisa al'ada ta larabawa suna zuwa dakin Ka'abah domin yin bautarsu tun zamanin jahiliyyah kafin aiko Annabi (S.A.W.W )a matsayin Manzo .
Fadimatu Bnt Asad ta tafi Ka'aba daidai lokacin da haihuwar ta kusantota, to, a lokacin da ta fuskanci ka'abah sai taji alamar naquda tare da ita. Sai tayi addu'ah da cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YAA ALLAH NA ROQE KA DA SUNANKA MAI GIRMA DA CEWA, KA SANYA MANI SAUQI A CIKIN NAQUDATA .‘’
Daga nan sai ta ga dakin ka'abah ya tsage ua bude, sai ta ji murya na cewa;
‘’ KI SHIGA !‘’ (domin lokacin dakin a kulle yake ).
Sai ta shiga, sai bangon ya koma yadda yake ya rufe.
Wannan abu ya faru a haban mutane da dama, sai Abbas (baffan manzon Allah )ya tafi da sauri zuwa wajen dan'uwansa Abu 'Dalib (A.S )ya ba shi labarin abinda ya faru ga matarsa. Da shike makullan ka'abah a hannunsa suke sai ya debo su yazo da sauri don bude dakin, amma yayi ya bude qofar ka'abar abin ya gagara . Har zuwa bayan kwana 3 sannan aka ga Fadimatu Bnt Asad ta fito da jariri ta qofar da ta shiga .
TAMBAYA
Shin, tsahon kwana ukun nan wa ke kawo mata abinci da abin sha?
AMSA
‘’ ALLAH NA AZURTA WANDA YASO BA TARE DA HISABI BA.‘’
Wannan abu,ya,baiwa kowa mamaki .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~27th February, 2020.