An Tattauna Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran A Vienna

Wakilan kasashen turai, da China da kuma na Rasha wadanda su ne suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran, sun sake tattaunawa yau a binrin Vienna kan makomar yarjejeniyar wacce ke tangal-tangal tun bayan ficewar Amurka daga cikinta.

  1. Karanata wasu labarai anan


(maasumah.com.ng Wakilan kasashen turai, da China da kuma na Rasha wadanda su ne suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran, sun sake tattaunawa yau a binrin Vienna kan makomar yarjejeniyar wacce ke tangal-tangal tun bayan ficewar Amurka daga cikinta.

Wannan dai ita ganawa ta farko tsakanin bangarorin tun bayan da kasashen turai suka gabatar da korafi kan Iran bisa da’awar cewa ta sabawa yarjejeniyar da aka cimma da ita a shekara 2015.

Yayin tattaunawar bangarorin sun amsa cewa lalle babu wani abu da Iran ta tsinta daga alkawullan da suka mata tun bayan da Amurka ta dawo mata da jerin takunkumai.

Amma duk da hakan sun jadadda mahimancin ci ga da aiki da yarjejeniyar, wacce ko ba komi tana tafiya da kudirin yana yaduwar makaman nukiliya a Duniya.

A nasa bangare karamin ministan harkokin wajen kasar ta Iran, wanda ya halarci taron na Vienna, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa har kulun kofofin kasarsa a bude su ke, idan har za a samar wa kasar hanyoyin cin moriyar yarjejeniyar.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post