🌹HAKIKANIN HIJABI GA MACE (1)
Abbagano ✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Kowane aiki na mutum yanada zahiri da badini, amma zahirin shine abinda muke iya gani a fili, badini kuma shine abunda ya shafi ruhi da zuciya.
Haka lamarin yake ta fuskacin hijabi. Hijabin zahiri shine manyan kaya da mace take sawa domin su lullube mata dukkan bangarorin jikinta tun daga kai har kasa.kuma aikata wannan abune mai sauki sosai.
Amma hijabin zuciya da ruhi yana bukatar zage damtse wurin mujahada , da zurfin imani.
Hijabin hakika, shine mace ta bayyana a cikin al'umma a matsayinta na mutum, ba a matsayinta na mace ba. Shiyasa kokarin sanya kaya masu jan hankali da kyalkyali ya saba da tarbiyyar da ruhi yake bukata.
Idan muka matsa gaba kuwa zamu ga cewa Ayyuka da dabi'un mace su suke bayyana nutsiwar ziciyarta, da rawar da zata taka a matsayinta na musulma.
Sau dayawa mace mai cikakken hijabi zata iya jan hankalinmu , a cikin kawayenta , saboda tafisu daga sauti, da dariya da shewa da wasanni. Shin tanaso tace mana dukda hijabin data sanya ita 'yar zamani ce wayayya?? Ko tana so ta kore tuhumar cewa ita bagidajiya ce wadda bata san inda zamani ya dosa ba?? Koko tana so tace ta samu 'yancin aikata abunda taga dama saboda takamar ta sanya hijabi??
Ni ina ganin cewa budurwar da bata kama kanta a cikin al'umma kamar tana so tace mana, ita mai hijabi ce a cikin masu hijabi, amma ballagaza ce a cikin 'yan zamani. Tana kokarin ta samu abokai masu yawa da yardar mutane
Abun takaici wannan dabi'ar tata zata bata mummunar fassara a cikin mutane.
Sannan ta rasa dukka biyu din,
Domin dan zamani bazai dauketa abun koyi ba, sannan masu addini bazasu dauketa abun koyi ba.
🌹HAKIKANIN HIJABI GA MACE (2)
Abbagano ✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Hijabi a ma'anarshi ta hakika , mace musulma, mai tsantsar kyawawan halaye, mai nutsuwar zuciya, tasan hadafinta, tasan hanyarta, tana kokari koda yaushe wurin tabbatar da abunda zai amfaneta da gidanta da al'ummarta, sannan tana kawata wannan ayyuka da hijabinta.
Zai iya yiwuwa kokarin jawo hankali da tsoron rashin yin aure da wuri ahine yake jawo wannan halaye ga mata masu hijabi, shiyasa take sakin jiki da kowa, yawan wasa da dariya wanda ya wuce haddi. To anan madai itace zatayi asara, domin hakan yana nuna cewa bata yarda da kanta ba, sannan mutumtakarta batada karfi. Al-muhimmu shi irin wannan dabi'a baya kawo girmamawa ga mace.
💜Yar uwata mai girma💜
Kada ki shagala da komai a rayuwa sai abu biyu :
1- na farko shine tambayar (MI YASA NAKE RAYUWA ), ba muzo duniya saboda muyi aure , ko kwalliya komu burge wasu ba.sai don mu samu yardar ubangidinmu, mubi umurninsa, mu hanu da haninsa, sannan mu dogara dashi cikakkiyar dogara. Da wannan zamu iya samun cikakkiyar shiriyar hijabin zahiri dana badini. Mu zama kamar tukunyar ubangiji , bamu bukatar komai a cikinmu sai yardarshi.
2- Abu na biyu shine kiji cewa zaki iya tsayuwa da kanki, ki cigabantar da mutumtakarki da kimarki. Idan kika aikata hakan to hankalinki zai kwanta , yakini zai wanzu a cikin zuciyarki, sannan hakan zai sanyaki mai jan hankalin dukkan wani dan adam, zai girmamaki.
A wannan lokacin mutane zasu soki.
Kowane yana fatan ki zamo uwar 'ya'yanshi , domin kin cancanci amicewa da yarjewa, kuma wannan kyawon ruhin naki da hasken zuciya zasu bayyana a fuskarki, a wannan mataki baki bukatar dukkan wasu kayan kwalliya domin jan hankalin wani da namiji.
