Asrar: Fa'idojin da ake samu, tattare da yiwa Manzon Allah (S) salati!


MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Daga Imam Ali as yana cewa: kowace addu'a katangaggiya ce ga sammai har Sai ma'abocin ta yayi SALATIN ANNABI S.
(Da'awatil rawandiy hadisi)

Faga Manzon tsira s. Yace: duk wanda biyan buqata yawuta gare shi to ya yawaita SALATI A GARENI domin Salati agare ni yana yaye bakin ciki da takaici, sannan yana yalwata arzuqi da biyan buqata.

SALATIN ANNABI S. Yana qara lafaya: daga Manzon Allah s. Wanda ya yi man Salati daya Allah ta'alah zai bude masa kofa daga kofofin lafiya

SALATIN ANNABI S. Yana kore shaidan daga Manzon tsira s. Lallai shaidanu guda biyu ne, shaidanun aljannu : ana  nisanta daga garesu ta hanyar karanta (LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZIM) da kuma shaidanun mutane su kuma ana neman tsari daga garesu ta hanyar SALATI ga ANNABI da ALAYENSA tsarkaka as

Yazo a riwaya cewa wani Mutum yazo wajen MANZON ALLAH S yana korafi akan talauci da yake damunsa, Sai MA'AIKI S. yace da shi: idan kana buqatar Allah ya azurta ka, to kayi Salati a gareni da alayena
(sawabul a'amaal 131)

Fatan Allah ta'alah shi gaggautaa kwato mana Jagoranmu daga hannun azzaluman Mahukuntan Kasar nan bihakki Sayyidatuna Zahrah sa.

Shaheed Muhammad Magaji

MA'ASUMAH
NIGERIAN
NEWS
UPDATES.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post