Da Dumi-Duminsa; Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta A Kaduna Sun Kashe Mutum Daya.

Shaheed Jawad Ameen Liman shahidin da aka harba yanzu haka a Kaduna.

Daga --Idishia Jos. 

 Yanzu haka labarin da ya fito daga Jihar Kaduna yana nuna cewa Jami'an tsaro had in guiwa da mutanen gari sun afkawa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na GARIN Kaduna a yayin muzaharar #FreeZakzaky da suke yi.


Jawad Ameen Liman Nan Take Yayi Shahada Sun Harbe shi a Kwakwalwa, an samu tabbacin rasuwan sa tare da jikkata wasu daga cikin almajiran Sheikh Zakzaky (H).

Yau Laraba 26/2/2020 yan uwa Almajiran Sayyed Zakzaky (H) na kaduna Sun fito muzaharan qara kira ga Gwamantin da ta Gaggauta sakin jagora sayyed zakzaky muzaharan wanda aka fara daga Gwamna road dake kan by pass da misalin karfe 6:00pm.


Aa cikin gabatar da muzaharan anzo dai dai wajan Masallacin Dahiru Bauchi dake kan By pass bayan an tashi yan uwa Sun fara tafiya kawai sai ga Yansanda nan sunzo zuwan su ke da wiya suka fara harbi kan mai uwa da Wabi cikin ikon Allah da yardan shi yan uwa suka kora jahiliyan bayan sun kora su sai ga yan qato da gora Sun fito suna gaba da addina suna gaba yansanda suna bayan su suna harbi.


Su kuma suna danno yan uwa cikin ikon Allah yan uwa suka danna su da yansanda daga baya suka qaro karfi suka danno yan uwa izuwa yanzu Sun harbi yan uwa da dama daga ciki akwai shahidi daya sannan Sun kama yan uwa da dama musamman sisters 


Ga wasu daga cikin hotunan da muka dauko muku a wajan 





Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post