Yan Sanda:/ IGP ya bayar da umarnin rufe ofisoshin rundunar SARS a fadin Najeriya

Babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin rufe wasu ofisoshin tawagar 'yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS) da ke fadin Najeriya. 

Babban mataimakin sifeton 'yan sanda mai kula da binciken manyan laifuka, Peter Ogunyonwo, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai gidan su dan wasan kwallon kafa, Tiamiyu Kazeem, da ke garin Sagamu a jihar Ogun. 

"IG ya bayar da umarnin a gaggauta rufe ofisoshin SARS," a cewar Ogunyonwo. Ogunyonwo ya cigaba da cewa, "alal misali, akwai irin wannan ofis a Ikorodu, akwai wani a Ijebu-Ode, akwai wani a Obada Oko, 

kuma dukkansu IGP ya bayar da umarni a rufe su ba tare da wani bata lokaci ba." Umarnin rufe ofisoshin na tawagar SARS na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da sukar rundunar 'yan sanda a kan muzguna wa da kisan 'yan kasa da wasu jami'an SARS ke yi a sassan kasa.  

Jami'an SARS Source: UGC

 A ranar Asabar 22 ga watan Fabarairu ne jami'an SARS suka kama marigayi Kazeem a garin Sagamu bisa zarginsa da cewa dan damfara ne ta yanar gizo. DUBA WANNAN: Badakalar N1.5bn: EFCC ta cafke tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abubakar Sanni, aboki ga Kazeen da suke tare a lokacin da SARS suka tare su, 

ya bayyana cewa 
Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
 jami'in SARS ne ya turo margayin daga cikin mota yayin da take tafiya bayan sun saka shi cikin motar domin tafiya da shi ofishinsu. Sai dai, rundunar 'yan sanda ta musanta hakan tare da bayyana cewa marigayin ne ya diro daga cikin motar a kokarinsa na gudu wa daga hannun jami'an SARS da suka kama shi. 



ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post