Bangarorin Dake Rikici A Libiya Sun Cimma Kudirin Tsagaita Wuta

Wakilan bangarorin dake rikici a kasar Libiya, sun cimma matsaya a Geneva kan wani kudirin da ya jibanci tsagaita bude wuta a kasar dake fama da rikici.

(ABNA24.com) Wakilan bangarorin dake rikici a kasar Libiya, sun cimma matsaya a Geneva kan wani kudirin da ya jibanci tsagaita bude wuta a kasar dake fama da rikici.

Kudirin kuma zai baiwa MDD, damar sanya ido kan shirin komawar fararen hula a yankunansu a cewar MDD.

Nan gaba ne wakilan bangarorin dake rikici a kasar da suka halarci taron tattaunawar na Geneva, zasu gabatar da kudirin ga jagororinsu domin dubawa, a wani mataki na share fagen wani taro a watan gobe domin sake komawa kan teburin tattaunawa domin shawo kan rikicin kasar, kamar yadda tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a Libiya (Manul) ta sanar a yau.

A makon da ya shude ne tawagar gwamnatin kasar ta Libiya dake samun goyan MDD, ta Fayez Al-sarraj da kuma bangaren Khalifa Haftar dake da rike da ikon gabashin kasar suka koma bakin tattaunawa a Geneva a shiga tsakanin MDD

Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post