Kotun Kaduna Ta Saurari Shugaban Gidan Yari Kan Hana M. Zeenat Ganawa Da Likitocinta

Kotun kolin jihar Kaduna, a Najeriya, ta saurari wani jami’in gidan yari, kan hana mai dakin jagoran harkar musulunci ta IMN, cewa da Malama Zeenat ganawa da likitocinta.

(ABNA24.com) Kotun kolin jihar Kaduna, a Najeriya, ta saurari wani jami’in gidan yari, kan hana mai dakin jagoran harkar musulunci ta IMN, cewa da Malama Zeenat ganawa da likitocinta.

Lauya, Gideon Kurada, ya kira jami’in ne lokacin da Shaih Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa suka sake bayyana a gaban kotu yau Litini a shari’ar da ake masu.

Kotun ta dau bukaci shugaban gidan yarin da ya yi mata bayyani kan yadda akayi aka hana likitocin Zeenat din su gana da ita.

Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Da ya ke karin bayyani kan lamarin Marshal Abubakar, mashawarci El-zakzaky, ya bayyana wa kotun cewa an hana Malama Zeenat ganawa da likitocinta na musamman wanda kuma ya sabawa umarnin kotun.

Yanzu dai an dage shari’a da ake wa Shaikh Zakzaky da mai dakin tasa har zuwa ranakun 23 zuwa 24 na watan Afrilun 2020 din nan, domin fara sauraren shaidu, kan zarge zargen da gwamnatin Kaduna ke masu.

An gurfanar da Elzakzaky da matarsa Zeenat a gaban babbar kotun ta Kaduna bisa tuhume-tuhumen kisan kai da taro ba da izni ba da kuma tayar da zaune tsaye da dai sauransu, zarge zargen da suke ci gaba da musantawa.
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post