Aklaq| Falalar Sallolin Ranar Asabar!!!



@Maasumah Nigerian News Update@

¶¶¶¶¶¶¶¶¶

    An ruwaito hadisi daga Manzon Allah cewa''Ana yin sallah raka'a hudu a kowace raka'a a karanta fatiha daya kulya ayyuhal kafirun kafa uku bayan ya kammala sai ya karanta ayatul kursiyu kafa daya.

       Falalarta
Wanda duk yayi wannan sallar
Allah (T) zai baiwa mutun ladan shahidi ga kowanne harafi daya karanta.

     Sallah ta biyu

An ruwaito daga Sayyid bn dawus daga Imam Hassan al'askari yace ya karanta a cikin littattafan iyayensa cewa''wanda yayi sallah raka'a hudu a ranar Asabar a kowace raka'a yana karanta fatiha daya da kulhuwallahu ahad da ayatul kursiyu kafa ɗai ɗai''.

      ®Falalarta

Wanda duk ya sallaci wannan sallar to Allah (T) zai sanyashi a darajar annabawa da shahidi da kuma salihan bayi.

   @ Maasuma Nigeria news update.@

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post