YADDA ZAKA KARE WHATSAPP NAKA DAGA YAN KUTSE (HACKERS)
*maasumah nigerian news update*
Tareda – Dan-Dalin Fasaha
Wannan nan hanyace mafi sauki da mai amfani da man hajar whatsapp zaibi dan kare kansa daga sharrin abokan mu yan kutse (hackers).
A farko dai zan baku wata shawara gata kamar haka
*Idan son samune a gaskiya kar kayi amfani da wani whatsapp app wanda bana asaliba ina nufin GB whatsapp ,FM Whatsapp, Bwhatsapp duk su ba asalin whatsapp bane ka nemi asalin whatsapp kayi amfani dashi.
Zaka iya yin duk wadan nan abubuwa da zan lissafa a ko wanne kalar whatsapp da kake dashi dan bada kariya gareshi kar makwamu sa su kwamushe maka baya nai.
Da farko dai zaka bude whatsapp app naka sai kaje kan (setting) sai ka danna da zarar ya bude saika je kan inda aka rubuta (Account) sai ka shiga da zarar ya bude sai ka wuce inda aka sa (Two-step verification) yana budewa a can kasa zakaga inda akasa (ENABLE) saika danna ka shiga zai nuna ma kasa numbers guda 6 sai kasa wanada bazaka taba mantasu ba zasuce ka maimai ta ida ka mai mai ta zai kai ka wani waje da zasu tambaye ka kasa Email naka saboda idan ka manta wannan numbers da kasa sai ka dawo dasu ta can in kayi niya sai kasa ka danna next ko kuma ka danna skip kawai sai kayi ok da zarar ya kamma to shikenan du sanda ka zo hawa whatsapp naka a sai ta nuna ma kasa wannan numbers kuma koda ka canza wata wayar ko ka chanza app na whatsapp naka ko wanna zai baka tsaro so sai wanda koda wani yayi hackin di whatsapp naka to bazai iya shigaba har sai ya sanya wannan numbers guda 6 da kasa a matsayin makulan whatsapp naka.
Nan muka kawo karshe wannan darasi mu hadu a wani na gaba.
Sunana –Aliyu idris mohd shi’a
Tags:
Yanar gizo
