Dalilin da yasa Kashe-kashen Aure da yawa Zawarawa Sukafi 'Yan Mata yawa a Duniyar Auren Hausawa

Dalilin da yasa Kashe-kashen Aure da yawan Zawarawa Sukafi 'Yan Mata yawa a Duniyar Auren Hausawa.

@Isma'il Abubakar Idris Katsina

Masu nazari da bincike sun gano Dalilan da yasa akafi yawan Kashe-kashen Aure fiye da kowace Kabila a duniya, A duk cikin kabilun Duniya Larabawa, Hausawa, Ibo, Yarbawa, Turawa, Gwarawa, Tubi, Filani, Inyamurai, Igala da sauransu na duniya babu kabilar da sukafi kowa kashe-kashen Aure da yawan Auri saki da tara Zawarawa kamar kabilar Hausawa 100%.

A duniyar Hausawa da zakabi unguwa-unguwa cikin garin ku idan zaka kilga tsakanin Zawarawa da 'Yan mata wane sukafi yawa, zakaga Zawarawa sunfi 'Yan mata yawa da kashi 80%, domin Hausawa basu dauki Aure da mahimmanci ba kamar yadda sauran Kabilu suka dauka.

Babban dalilinda ya haifar mana da wannan matsalar shi ne ÷ Babu kabilarda ake Aure da sauki kamar kabilar Hausawa domin a cikin Hausawane zakaga Anbayar da Sadakin Mace Budurwa #20,000, wannan dalilin yasa da Matar bahaushe tayimasa abu kadan zakaga ya saketa sabida yana ganin auren wata bazaimasa wahala ba.

Yadda za'a magance wannan Babbar matsalar Auri saki dake cikinmu Hausawa ÷ A duniyar Hausawa madamar anaso a magance wannan matsalar sai dai a maida Salakin Budurwa #1,000,000 ko 500,000, tawannan hanyar ne kawai za'a magance wannan matsalar.

Dalili shi ne ÷ Dukkan wanda yaga yabiya Makudan kudade kamar #1,000,000, ko #500,000 yayi aure bazai yarda laifi kadan yasa  yasaki matarsa ba! domin daya tuna infa yasaki matarsa saiya kara neman Kudi #1,000,000 ko 500,000 sannan yakara wani auren bazai yarda ya gaggauta saki Matarsa ba.

Yanzu idan mutum yaga bayada kudi zakaga ya tattago Aure domin yana ganin sadaki #20,000 ne, 'yan uwansa da abokai da dangin Uwa dana Uba zasu hada masa wasu makudan kudade zaiga ai wannan wata hanyace ta samin kudi ( Income), da anyi auren watanni kadan sun rabu ya saketa.

Ta wannan hanyar ne kadai za'a iya magance wannan matsalar
 da ta addabemu cikin  kabilarmu ta Hausawa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post