*DAKE NAKE SISTER* *KADA KIYI MU'AMALA DA KAWA MAI WADANNAN SIFFOFIN!*

Ma'asumah Nigeria News Update
Writing by M.N.U 030

Kada kiyi mu'amala da kawar da bata da tarbiya, yana da kyau kisan da kawar da zakiyi mu'amala. Wata kawar zata boye maki munanan dabi'unta, yayin da wata kuma zata bayyana maki su karara. Abinda nake so nace anan shine ita mummunar kawa dabi'unta sun kasu kashi biyu,

Akwai bayyanannu da kuma boyayyu. Kawa wadda ta kasance mai munanan dabi'u na bayyane, itace wadda da kun fara mu'amala da ita cikin sauki zaki fahimci halayenta, kuma ke kina iya canza ta, ta gyara dabi'unta cikin hikima. Amma idan itama tayi nisa bata iya sarrafuwa,kuma da zaran ta fahimci kina son rabata da dabi'unta ne, zatayi kokarin rabuwa dake ta nemi wata.

Daga cikin dabi'un mummunar kawa na zahiri, akwai masu wahalarwa domin canzasu bazai maki sauki ba cikin kankanin lokaci. Na farko zaki sameta bata da tarbiyyar harshe, bata tsoron furta kowace irin kalma, agaban ko wanene. Addininta bai dametaba bare tayi kishinsa,

Magulmaciya,makira,Shu'uma,masharranciya,mai yawan hassada,tsegumi da munafurci. Bata shakkar iyayenta bare taga girmansu,musamman idan talakawa ne. Bata da kamun kai bare taji kunyar maza,mai tsananin son abin duniya,Wanda kan iya sawa ta zama barauniya. Yawan roko musamman a wajen maza, Kalmar baza bataimata wuya ko jin kunyar ta Wanda hakan zai iya jagorantar ta zuwa aikata zina.zata iya kasancewa 'yarmaye,zata iya kasancewa ma'abociyar kallon tsiraicin Mata,ta hanyar hoto,ko Fina-finan batsa! Wanda hakan zai iya sawa ta zama tana neman mata.


*ZAKI IYA CANZAWA KAWA WADANNAN DABI'UN NATA*


Idan ya kasance bata da masaniya akan addinin ta kuma bata damu da tambaya ba,ko zuwa makaranta,kuma bata san hadarin dake tattare da hakan ba. Ibada bata dameta ba,bata da tsari a rayuwar ta,yawan surutu musamman a lokutan da ba'a da bukatar sa, bata da tsabta ta kowane janibi,rashin kamun kai Wanda zai iya janyo Mata raini,musamman ga na kasa da ita,bata damu da Neman ilimi ba kuma ga yawan karya.


Sukuwa siffar mummunar kawa na zahiri sun hada da:- girman kai da dagawa, tare da jin cewa ita ta isa,bata da tausayi bare imani,damuwarta kawai ta dameta bata damuwa da damuwar wani. Boyayyun siffofinta kuwa sune masu wahalar ganewa,masu wadannan dabi'un sunada matukar wayo da kaifin basira,ta yadda zasu dinga cin dunduniyar kawa ko aminiya ba tare da tasani ba.illarsu yafi na makiyin zahiri.


Sune zaka gansu sunfi kowa iya nuna maka so da kauna,akwai nuna damuwa cikin damuwar ka,ruwan alkhairi da faran-faran kan saye zuciyar kawarsu,suna kokari sosai don ganin sun san sirrinki,da duk wani boyayyen al'amarinki, suna kokarin biyayyar iyaye,dangi,da makusantanki,a wani salo na yaudara da kokarin bankado sirrinki.
Wadannan kadan kenan daga siffofi da dabi'un mummunar kawa. Ya ragemana yin tunani don neman cikakkiyar Aminiyar da zamu rayu da ita, Allah yasa mu dace.

-----------------------------------
Sakina Ahmad kazaure

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post