Yadda Aka Jefa Almajiri Dakin Gasa Burodi A Gombe

Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.

Wani yaro dan shekara goma na can kwance rai kwakwai mutu kwakwai a garin Bajoga da ke jihar Gombe, sakamakon kona masa kafafuwa, bayan jefa shi cikin murhun gasa burodi da ake zargin wani manajan gidan burodi ya yi.
Bayanai sun ce mutumin ya zargi almijirin ne da satar masa burodi.

Kungiyar Muryar Talaka, mai kare muradun talakawa a Najeriyar, ta shaida wa BBC cewa, an kama wanda ake zargi da azabtar da yaron, amma daga bisani aka sake shi, yayin da yaron ke can kwance magashiyan cikin ciwo a gida.

Ahmed Sulaiman, wani dan kungiyar Muryar Talaka reshen garin Bajoga a jihar Gombe ya shaida cewa ya ziyarci yaron da al'amarin ya faru a kansa wanda malamin makarantar allo ke jinyar sa. Ahmed ya ce "abin da ya faru shi ne manajan gidan burodi ya zargi yaron da satar masa burodi inda ya jefa yaron cikin dakin gasa burodin.

Jim kadan sai ya fito da shi amma sakamakon ganin babu abin da ya samu yaron sai ya sake mayar da shi dakin gasa burodin, inda bayan fito da shi kamannin yaron suka sauya." Jagoran Muryar ta Talaka ya kuma yi zargin cewa mutumin da ake zargi da aikata wannan laifi ya tsira daga hannun 'yan sanda bayan da wani babban mutum ya yi belin sa.

Har wa yau, kungiyar ta Muryar Talaka ta ce tuni aka yi wa manajan gidan burodin takardar shaidar tabin hankali. Sai dai lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Gombe, SP Mary Malum ta ce ba ta da bayani amma idan sun sami bayani za su tuntube mu.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post