Me Yafi Cutarwa Tsakanin Soyayyar Qarya Da Kuma Qiyayyar Gaskiya??@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @

A ZATONA YAUDARA YA FI CUTARWA

Wani zai zaci wannan tambaya ba da ma'ama , ko kuma yayi zaton an yi ta ne kawai don nishadi, amma a zahiri akwai darasi cikinta.

Sau da yawa wasu na fadawa cikin tarkon soyayyar yaudara, daga mata ne ko maza , wanda a qarshe akab cutu fiye da yadda ake zato.

Daga cikin illar soyayyar yaudara ita ce, duw wanda ya amince maka da cewa yana sonka da gaske, to, za ka aminta da shi ta hanyar bayyanar masa da dukkan wata damuwarka ko wasu sirrikanka, shi kuma masoyi na yaudarar zai riqa watsa wadannan sirrikan naka ga wasu wadanda wataqila ma abokan gabanka ne.

Idan mace ce ke yi maka irin wannan soyayya za ta kasance mai yawan bayyanar maka da so na zahiri ta yadda za kaga babu abinda za kayi mata wanda zai gamsar da ita cewa kaima kana sonta da gaske , a dalilin haka sai kayi ta yin hasarar abinda ka mallaka don farranta mata,, a qarshe kuma sai ta juya maka baya wanda hakan kan iya zama sanadin kamuwa da hawan jini ga masu qarancin tawakkali.


Sannan idan mace ce ta gano cewa soyayyar yaudara ake yi mata, to, idan wani yazo mata za ta iya aminta da shi  ba tare da ta sake sake har a barta a igiyar ruwa ba, wato ta wayi gari cikin baqin cikin rasa shi alhali ta qi aminta da masoyinta na gaskiya ba.

Ita kuma qiyayya ta zahiri na da sauqi , domin duk wanda ka san maqiyinka ne ka kanyi taka-tsantsan da shi don gujewa sharrinsa gare ka.

Sannan kuma ba za ka sami dama ta hasarar dukiyarka gare ta ba, ko kuma ba za ki sake jiki da shi sosai ba don kin san maqiyinki ne , wannan kuma ga matan da suka sami kansu cikin jarrabawar son maso wata kenan.

Shi maqiyinka ns gaske ko da ba ta hanyar soyayya bane, ka san yadda za ka kaucewa sharrin sa don kada ya cutar da kai.

Saboda haka nake gani maimakon ka hadu da masoyi ko masoyiya ta yaudara gara Allah ya haka ka/ki da magiyi na zahiri.

Tare da Ado Isah Guda .

08126385470-08137925034

~12th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post