Wajibi Ne Yara Su Riƙa Ganin Girman Manyan Cikin Su!!!

DAGA KHUDUBOBIN IMAM ALI (A.S )!!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Idan ka kalli halayya ko dabi'un mafi yawan matasan wannan zamani sai abin ya sa ka kuka saboda rashin biyayyarsu ga na gaba da su.

Wannan mummuniyar dabi'ar ana samunta cikin dukkan wata tafiya ta addini. Sai ka tarar yara mata na raina tarbiyyah da qoqarin mahaifansu mata cikin addini. Su kuma yara maza na ganin tunaninsu, hankalinsu , da riqo da addininsu ya fi na manyansu da suka karantar da su har ma suka san wani abu na addini .

Wasu manyan kuma basu san yadda za su yi mu'amala da yara a matsayin su na wadanda ake tarbiyyantarwa ba. Wannan dalili yasa ka ke ganin matsaloli na aukuwa cikin kowacce tafiya.

Ya zo cikin khudubar Imam Ali (A.S )inda yake cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ YARAN CIKINKU NE YA KAMATA SU BI MANYAN, (ba manya su bi yara ba ), YAYIN DA MANYANSU KUMA SU ZAMA MASU KYAUTATAWA YARA (ba cutar da su ta hanyar ba su mummuniyar tarbiyya ba ). KA DA KU ZAMA KAMAR MUTANE MARAR SA KUNYA NA LOKACIN JAHILIYYAH WADANDA BA SA CUSA KANSU CIKIN ADDINI KO KUMA SU YI AMFANI DA HANKULANSU AKAN AL'AMARIN UBANGIJI .

SU (yara )KAMAR FASA QWAI NE A CIKIN SHEQAR TSUNTSU MAI HADARI (cutarwa in an bar su ), DOMIN KUWA FASA QWAI ZAI ZAMA KAMAR ABU MARAR KYAU (in aka dubi aikin ), AMMA BARINSU (qoyin tsutsaye masu cutarwar)ZAI IYA JAWOWA (tsuntsayen )SU SAMAR DA 'YA'YA MASU HADARI .‘’

  (NAHJUL-BALAGHA, SH:323).

Wato barin irin wadannan  matasa kan wannan mummuniyar tarbiyyah  zai iya zama hadari cikin kowacce  tafiya . Saboda haka wajibi ne kan manyan cikinsu su cigaba da basu tarbiyyah ko da kuwa yaran na zaginsu , kuma su riqa jawo su a jika ta hanyar kyautata musu ba nisantar da su ba.

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da  Ado  Isah  Guda.

       08126385470

~20th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post