Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Wani shugaban makarantar Sakandare a Legos, Mista Samson Adeyemo, ya amsa laifin sa a gaban kotun hukunta masu aikata laifuka da ke Ikeja, inda ya amsa cewa lallai ya rika saduwa da wasu daliban makarantar na shi ‘yan tagwaye biyu masu shekaru 17 da haihuwa. Shugaban makarantar mai suna Adeyemo, mai shekaru 41 da haihuwa, yana zaune ne a gida mai lamba 8 da ke kan titin Odesanya Street, Abule Egba, Lagos, shi ne kuma shugaban makarantar Sakandare ta Legati College, Abule Egba.
Yana fuskantar tuhumomi ne guda biyu na lalata daliban na shi biyu. Da dan sanda mai gabatar da kara, Mista Oshodi, yake yi masa tambayoyi a jiya, wanda ake karar ya amsa cewa; “Da gaske ne na rika kwanciya da Yarinya ta farko, da kuma ta biyun. Amma a zahirin gaskiya mun kulla aure ne da Yarinya ta farkon. Sai dai ba a Coci ne ko wajen masu daura aure ne aka daura mana auren ba. amma dai na sami amincewar ta, iyayenta kuma suna da masaniya,” in ji shi.
Ana yin aure ne a tsakanin namiji da mace domin rayuwa. Abin da ke a tsakani na da Yarinya ta farko aure ne, mutane suna zuwa Coci ne ko wajen masu daura aure domin bukin aure kawai. Mun fara soyayya da Yarinya ta farko ne tun a shekarar 2016, amma sai a shekarar 2017 ne na fara kwanciya da ita. Amma ban fara yin wata alaka da Yarinya ta biyu ba har sai da na zauna da mahaifiyar su, na kuma fara kwanciya ne da Yarinya ta biyu din a bayan mun zauna da mahaifiyar nata.
Sai dai ya karyata batun zargin da ake yi masa na cewa ya saba yana kwanciyar lalata da sauran daliban makarantar na shi mata. Tun da farko, wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya yiwa Yarinya ta farkon ciki ne a lokacin da aka danka amanarta a hannun sa. Lauyan wanda ake tuhumar, R. O. Akande, Adeyemo, ya ce Yarinya ta biyu din ta soma yin kishi ne a lokacin da ta fahimci alakar da ke a tsakanin ‘yar’uwarta da kuma malamin na su.
Yarinya ta biyu ta zo gare ni tana kokawan me ya sanya sai ‘yar’uwarta ce zan je ina nema. Na shaida mata cewa ita din ne nake so na nema. Sai ta ce mani ita ma tana da samari, amma kuma tana so na saboda ina son ‘yar’uwar tagwacin ta, in ji shi. A shekarar 2017 da Yarinya ta farko din ta samu juna biyu, sai na yi nufin na dauki nauyin komai nata, amma sai iyayenta suka ce ba su yarda ba, suka kuma dage a kan cewa sai a zubar da cikin.
Ni kuma na ki saboda ina son abin da za a haifa din, ina ma kuma son na auri Yarinya ta farko din. Na ba ta wasu kudade domin ta kula da kanta, amma sai iyayenta suka kwace kudin daga hannun ta, suka kuma zubar da cikin.
Shugaban makarantar yace uban yaran ya bukace shi da ya biya naira 200,000 ko kuma ya fuskanci hukunci. “A bayan kwanaki biyu da yin hakan ne dan’uwan uban na su wanda ake kira da suna Kayode, wanda kuma aka fi kiransa da Kokoro, ya jagoranci wasu zauna gari banza suka zo suka lakada mani duka a ranar 26 ga watan Afrilu, 2017, sai kuma shi kayode din ya kira ni domin na zo na sa hannu a kan takardar alkawarin cewa ‘Yan tagwayen za su karbi takardar shaidar su ta WAEC,” in ji shi.
Sai na je na same shi ba tare da sanin cewa ya shirya mani tuggu ne ba, a nan take ya danka ni a hannun ‘yan sanda. A cewar mai gabatar da kara, shugaban makarantar ya lalata dukkanin ‘yan tagwayen biyu ne a cikin makarantar da ke Anguwar Abule Egba, wani lokaci a shekarar 2016. Alkalin kotun ya dage sauraron karar har ya zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu. Da ta ke bayar da shaida a gaban kotun, ‘Yarinya ta farkon wacce shugaban makarantar ya yi wa ciki, ta shaida wa kotun cewa, Adeyemo din yana da wani gadon tafi da gidanka ne a cikin ofishin sa wanda a kansa ne ya rika kwanciya da ita.
Ina SS1 a lokacin da abin ke faruwa. A ranar da abin ya fara aukuwa ina zaune ne a cikin ajinmu sai ga shugaban makarantar ya shigo ya na tambaya ta ko malaminmu ya na nan ne. Sai na ce ma shi ba shi nan. “Daga nan sai ya ce na biyo shi zuwa Ofishin sa. a lokacin da na isa Ofishin na shi ne sai ya fara kira na da sunaye masu dadi inda daga bisani ya fara cire mani tufafin makarantar da ke jikina.
Har dai ya kwanta da ni, ya kuma umurce ni da kar na kuskura na shaida wa kowa. “Daga nan ne ya ci gaba da kwanciya da ni har na tsawon wani lokaci, har sai da na sami juna biyu. Ni ban ma san cewa na sami juna biyu din ba, har sai da wata makwabciyar mu ta lura da wasu canje-canje a jikina ta kuma sanar da mahaifiya ta. “Da mahaifiyata ta tuhume ni ne sai na shaida mata cewa shugaban makarantar mu ne ya ke kwanciya da ni a cikin Ofishin s
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya