Tirqashi| Saudiyya Ta Buga Quranin Yahudawa!!!


@Ma'asumah Nigerian News Update@

Kafar Middle East Monitor, wacce a taqaice ake kira MEMO, a jiya Talata, ta ruwaito cewa, Saudiyya ta wallafa Qur'ani na musamman da harshen Yahudanci, wato Hebrew. Kamfanin King Fahd Complex da ke Madina ya wallafa sabon Qur'anin.

MEMO ta ce an samu sama da kurakurai 300 a cikin Qur'anin da suka danganci rashin fassarar wasu ayoyi da gangan tare da goge wasu ayoyin gaba daya. Kafar ta ce akwai ma wuraren da aka goyi bayan haramcciyar qasar Isra'ila kan da'awarta ga Palasdinawa da Masjidul Aqsa.

Fassararren Qur'anin ya ciccire sunayen Annabi Muhammad (sawa), ciki har da ayoyin Isra'in da Manzon Allah (sawa) ya yi daga Makka zuwa Masjidul Aqsa cikin dare guda kamar yadda ya zo a surar Isra'i.

Kafar ta MEMO ta ce, "Wannan kwafen Qur'ani zai iya sa Yahudawan tunanin cewa ashe babban littafin Musulunci Qur'ani yana goyon bayan Yahudawan ne."

Kafar ta ce, ta samu labarin wannan kwafe na Qur'ani ne daga kamfanin dillancin labaran Palasdinawa mai suna Shehab News Agency.

Wannan ke nan...

Kira Ga Wahabiyawan Arewa

Wannan labari, idan har ya tabbata gaskiya ne, to abin baqin ciki ne ga duk wanda ya ce La'ilaha illallah Muhammad Rasulillah! Domin cin zarafin addininmu ne da gangan.

Duk da cewa Shi Allah ya yi alqawarin kare littafinsa, amma kasancewar an ma samu yunqurin sauya wasu ma'anonin littafin kuma daga qasar Musulunci wacce ke kan aqidar Wahabiyanci, dama ce a gare ku, ya ku Wahabiyawanmu na Arewa, da yakamata ku yi zaman dirshan don karatun ta-natsu a kan yadda kuke mu'amala da Musulman da suka saba da ku a aqida, kamar Sufaye da 'yan Shia.

Yawan kafirta Musulmi da jingina rashin yarda da Qur'ani ga wasu, ababen da kuke yawan yi ba bisa dalili qwaqqwara ba, to, wannan labari, in har ya tabbata, abin kunya ne gare ku kuma ramuwa ce da Allah ya yi wa wadanda kuke uzzirawa.

Allah ya sa ku gane, kuma ya hada kanmu don fuskantar haqiqanin matsalolinmu na gida da waje.

 Daga Wakilan mu na Bauchi
Tare da Ado Isah Guda
29/01/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post