@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AKAN HAKA MA YA TAYAR DA ANNABAWA (A.S )DA MUJADDADAI
Zabin Allah ne da kuma baiwarsa ga bayi yake tayar da zababbun cikinsu don su gargadi al'umma game da ranar gamuwa ta qarshe, wato ranar tashin qiyama.
Ita ce ranar da duk wani azzalumi zai qasqanta , mai shan giyar mulki yasan shi ba komai bane.
Rana ce da duk wasu masoyan azzalumai za su guje , kuma babu wata biyayyar da za suyi musu irin ta duniya .
Allah (T )na cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ (Allah )MAI 'DAUKAKA DARAJOJI (muminai )MA'ABUCIN AL'ARSHI , YANA JEFA RUHIN (addini )DAGA AL'AMARINSA AKAN WANDA YA SO DAGA BAYINSA, DOMIN YA YI GARGADI KAN RANAR GAMUWA (na azzalumai da wadanda aka zalunta). ‘’
RANAR DA(azzalumai da masu goya musu baya )SUKE BAYYANANNU, BABU WANI ABU (na zalunci )DAGA GARE SU WANDA YAKE IYA BOYUWA GA ALLAH . (Allah yace;)‘’ YAU MULKI GA WA YAKE ?‘’ YANA GA ALLAH (ne kadai )MAKADAICI MAI TILASTAWA (dukkan wani azzalumi da fajiri zuwa wuta ).
(Sai Allah yace )YAU ANA SAKAWA KOWACCE RAI A GAME DA ABINDA TA AIKATA, BABU ZALUNCI A YAU. LALLE ALLAH MAI GAGGAWAR HISABI NE (kan dukkan wani jabberi ).
KUMA KA (qara )YI MUSU GARGADI KAN RANAR (sakamakon)MAKUSANCIYA , A LOKACIN DA ZUKATA (na azzalumai da miyagun mutane )SUKE MASU BAQIN CIKI GA MAQOSA (na ganin sakamakon da za ayi musu). BABU WANI MASOYI GA AZZALUMAI (a wannan rana ), KUMA BABU WANI MAI CETO DA ZA A YIWA 'DA'A (wajen cetonsu ).‘’
(Suratul-Ghaafir, aya ta 15-18).
Sai dai duk da wannan gargadi nasa ba zai hana azzalumai, fajirai da mahassada shiga wuta ba. Kamar dai yadda Annabawa (A.S )da sauram mujaddadai ba su hana su shiga ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare Ado Isah Guda.
~29th January , 2020.
Tags:
Jagoran Gaskiya