Tun shekarar 1969 aka gano cutar Lassa a Arewa-maso-Gabas din Najeriya a wani gari da ake kira Lassa, don haka ta samo sunanta na “Lassa Fever”. Cuta ce da kusan duk shekara sai an yi ta a lokutan sanyi ko bazara a gurare daban-daban na Najeriya, musamman a kauyukan da ake noma sai ake kona gonaki ko bude hanyoyinsu don tunkarar damuna. A wadannan lokuta ake samun bearaye suna guduwa daga gonakin suna shiga cikin gari neman abinci tunda an debe kararen da suke ci. Wadannan beraye su ne suke kai cutar lassa cikin gidaje.
Cutar Lassa tana da hadari kamar na Ebola. Duk da Ebola tafita saurin yaduwa amma kuma cutar lassa tafi zama. Matsalar da ake samu ita ce gwamnati ba ta fiye shiryawa cuta ba sai ta zama annoba, ita kuma al’umma ba ta zuwa asibiti har sai cutar ta zama babba. Tun asali gwamnati ya kamata a ce ta shiryawa cutar nan da wayarwa tun kafin zagayowar bazara domin hakan ne kawai rigakafin cutar tun da an ce ita ba ta da riga-kafi irin na magani mai inganci. Shekara sama da 40 ana abu daya amma har yanzu gwamnati ta kasa fito da sahihiyar hanyar maganinsa!
Al’umma kuma ya kamata ta sani cewa duk wani daga cikinta da ya ji zazzabi kowane iri ne to ya tafi asibiti. A matakin farko na cutar nan an ce tana kama da “Malaria” ko “Typhoid” kafin ta karasa gun manyan alamominta na zubar da jini a kafofin dan Adam kamar ido, baki, hanci da kunne. Idan ka je asibiti aka ce maka ba cutar lassa ba ce to sai a baka maganin zazzabin da yake damunka. Amma idan ka je aka ce maka ita ce to za a iya baka magani a matakin farko domin a dakatar da cutar don ka samu shiga kaso 15 cikin 100 na mutanen da suke samun lafiya bayan samun cutar.
Allah ya sa mu dace.
✍️ALIYU DAHIRU ALIYU
Tags:
Daga marubata