Yi shere domin wasu su Amfana
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @Shafi domin kai da Al`ummar ka
AIKINKA SHI ZAI FASSARA KAI WANENE .
A tunani irin nawa shine, ya kamata duk wanda ya ji daga kai tsaye daga Annabi (S.A.W.W )ya fi kiyaye abinda ya ji a aikace fiye da wanda labari ne kawai ya riske shi.
Haka zalika, duk wanda ya ji maganar gaskiya daga jagora kai tsaye , shi ya fi cancanta ko kamata ya aikata abinda ya ji ko ya yake ji daga gare shi, sai dai ashe abin ba haka yake ba.
Akan sami qalilan,ne ke iya kiyaye wannan magana, mafi yawan mutane kuma sai suyi watsi da abinda suka ji, su aikata abinda zuciyarsu ta riya musu. Sai kuma ka samu daga cikin wadanda labari ne ya riske su su fi kiyayewa da kuma bin abinda labari yazo musu da shi.
Ba zai taba zama abin mamaki ba don ka ga wani ya zama dan ga-ni-kashe ni wajen bin maganar Manzon Allah (S.A.W.W )wanda wasu su kayi watsi da ita alhali sun ji kai tsaye daga gare shi.
Hakan ya tabbata cikin wani hadisi da aka kawo dangane da Khudubarsa (S.A.W.W )ta qarshe ga al'ummarsa . Cikin Khudubar yake cewa;
…
‘’ LALLE JINANANKU DA DUKIYOYINKU DS MUTUNCINKU A TSAKANINKU HARAMUN NE, KAMAR DAI HARAMCIN WANNAN RANA TA KU, CIKIN WANNAN WATA NA KU, CIKIN WANNAN GARI NA KU. WANDA YAKE NAN YA ISARWA WADANA BAI NAN (for those are present to deliver it to those who are absent ). DOMIN AKWAI YIWUWAR WADANDA KE NAN SU ISARWA WADANDA ZA SU FI SU KIYAYE SHI (a aikace ).‘’
(BUKHARI , HADISI ME LAMBA 67).
Yaa Allah ka tabbatar damu kan abinda labarinsa yazo mana ns gaskiya .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
~25th January , 2020.
Tags:
Makaranta