Boka Ya Yi Wa Matar Pastor Ciki.

Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos. Wata matar Pasto ta sami ciki wanda a halin yanzun yake a cikin watan sa na biyu, sai dai kuma batun shi ne cikin na wane ne? Boka da ake Magana dan asalin garin Osha ne a yankin na Onitsha, bokan wanda har-ila yau ya fi shahara da sunan da ake kiransa da shi na, Ebeano-Dike. ‘Yan kasuwa manya da kanana, maza da mata da ma sauran al’ummar yankin suna ziyartar sa matuka domin neman ya yi masu magani da asiri a kan abubuwa mabambanta, sai dai kuma wani abu da ba a sani ba shi ne irin soyayyar da ke a tsakanin sa da matar Paston cocin garin wacce take ziyartan sa domin neman samun juna biyu. Tabbas da sanin Pasto din ne matar na shi take ziyartar Bokan, sai dai shi abin da ya sani shi ne kadai tana zuwa ne domin neman masu maganin da matar na shi za ta sami juna biyu, a bayan shekaru da suka jima suna jira. Amma Allah bai ba su juna biyun ba, wanda hakan ne ya sanya suka yanke shawarar zuwa wajen boka Ebeano-Dike, domin neman taimakon sa. Hakane, an samu nasara matar Pasto ta sami juna biyu, amma ta kuma tabbata cewa cikin da ta samu na Bokan ne. A yanzun haka dai matar Pasto tana ta faman samun tsangwama daga al’ummar garin, inda ma suke neman Pasto din da ya saki matar na shi domin ya sake auren wata matar ta daban, a bisa abin da mutanan garin suke kiran matar Paston da cewa ita mayya ce kuma mazinaciya. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post