
Daga Wakilin Mu --Idishia Jos.
A ziyarar da aka kai wa Sheikh Zakzaky a ranar Alhamis 'din da ta gab, Ofishin Sheikh Zakzaky ya tabbatar da labarin ziyarar. Wannan yana biyo bayan shafe fiye da kwanaki 50 tin bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta tsara maida su Malam gidan Yari (Prison) domin kulla wani makirci kan haka.
Sheikh Zakzaky sun bayyana irin yanayin jikin nasu musamman guba da harsashai dake jikin su. Dama me kake tsammanin d me jinyar da ba'a kaishi a Asibiti ba? Lalle babu abinda ya canza babu kulawa ko ta kara balle ta dole. Mutum irin Malam Zakzaky daya bawa shekaru 60 baya yana fama da munanan raunin harsasai masu guba yaya yakeji?
Wannan yana nuna suna yunkuri ne na kisa a fakaice. In ba haka ba Ofishin ya tabbatar da cewa tun bayan mayar da Sheikh Zakzaky Gidan Yarin na Kaduna had yanzu babu wani likita da aka Bari domin yazo ya duba lafiyansu.
Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat sun shafe sama da shekaru 4 jikin su da harsasai na bindiga tun bayan harin ta'addanci da Gwamnatin Buhari tayi a ranar 12 Ga December 2015.
Sati Biyu da suka wuce Gwamnatin Kaduna tana alwashin cewa ita bai zata saki Sheikh Zakzaky ba, ta bangaren Harka Islamiyya kuwa sun yi taron Manema Labarai cewa Wannan Yunkuri ne kawai na kisan kai ga sheikh Zakzaky.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.