SAKO MAI KARFI ZUWA GA AMERIKA DAGA IRAQ


Cincirodon Al'ummar kasar iraqi sama da miliyan ne suka fito da safiyar nan ta juma'a 24/1/2020, nuna kin amincewarsu da ci gaba da zaman Amerika da sojojinta a kasar tasu. 

Suna fadar lallai dole amerika ta fice daga iraqi a jerin gwanon nasu mai taken #LeaveToLive. Wannan zanga-zanga mai karfin gaske ta barke ne bayan soke duk wani yarjejeniya da alaka ta tsaro da Ayatullahi Muqtadha Sadr yayi da amerika. Hakan ya biyo bayan kisan Gen. Qasem Sulaimani, da Al-muhandis.

Titunan Baghdad ne suka dauki Al'umma ba wajen saka tsinke, dauke da kwalaye da hotunan kiran amerka da ta janye sojojinta idan tana so su rayu. Haka wasu sunyi dan butum-butimin shugaban kasar amerika Donald Trump tare da rateye wuyansa a jikin wani katako.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post