@Ma'asumah Nigerian News Update@
KAURIN HIJABI
-Tufafi yazam mai Kauri, ta yadda bazai bayyana sura ko siffar dirin jikin mutum ba, ya zama dole mu tunasar da ƴan uwanmu Mata Hijabi bashi ne saka dukkan wani kalan yadi don a rufe jiki ba. Yadi sara-sara ko wanda ya tsuke ta yadda zai iya bayyana surar jiki da siffar dirin jiki ya haramta a sakasu.
-Manzon Allah (S) yace a wani hadisi, "Matayensu zasu ke ado a tsirara, kayukansu kamar tozon durƙusasshen raƙumi, Allah ya tsine musu, dama cen su tsinannu ne".
-Manzon Allah (S) akan ganin wata amarya da matsattsen kaya yace, "Mace wanda tai ado kamar haka, batai Imani da Suratun Nur ba". Ado kar yazam ɗaurarre/matsattse ta yadda zai bayyana lanƙwasa ko siffar dirin mace.
Uwa Uba Bayyana Sura.
1-Manufar sanya sutura shine don rufe hanyar Ado, wannan sannan nen abu ne ado kar ya zama irin kwalliyar da zai ke ɗaukar hankalin masu kallo zuwa ga mace.
-Ado bazai buya ba ga masu sanya tufafin da yake sanya mutane su juya idonsu zuwa ga wanda ya sakasu, irin wannan adon aka haramta a cikin Wata ayar Qur'ani; "Kada ku ƙawata kanku da kwalliya irinta jahilan farko".
2-Kada mace tai ado da sannanen kayan adon maza, ko kuma akasin haka. Manzon Allah (S) ya tsinewa maza masu adon mata da kuma mata masu adon maza.
3-Ado kada ya zama ado mai tsada, alfahari ko girman kai. Sanya sutura wuce kimar datti, ko tufafi mai ƙarko, don a nuna musu kai a cikin Al'umma bai halatta ba.
-Nuna ado da alfahari ba daidai bane a Muslunce, Manzon Allah (S) yace, "Duk wanda yai ado mai daraja a wannan duniyar, Allah zai mishi ado na tozarci a ranar Alƙiyama, sannan a saka shi cikin wuta".
Wa iyazu billah...........
-Insha allah zan ƙarisa rubutun in Allah ya aramin lokaci.
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈