
Daga Wakilin Mu --Idishia Jos.
Hukomin tsaro a Iraki sun tabbatar da saukar manyan rokoki a kusa da sansanin sojojin Amirka da ke Bagadaza babban birnin kasar.
An ji karar fashewa a yammacin gabar Tigris yankin da yawancin ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a Iraki.
Babu wadanda suka dauki alhakin sabbin hare-haren rokokin kan barikin sojojojin Amirka da ke Irakin zuwa yanzu.
Sai dai dama ana zaman dar-dar na yiwuwar harin fansa daga Iran tun bayan da Amirka ta kashe janar Qassem Soleimani, wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jamus ta dawo da atisayen sojinta a Iraki bayan dakatarwar da ta yi.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.