@Isma'il Abubakar Idris Katsina.
Harisawa 'ya'yana ne, nine Shugabansu. Harisanci aiki ne domin taimaka wa Al'umma kamar yadda Jamhuriyyar Muslunci ta Iran ta kir-kiri (Imam khumaini Relief), domin taimakon Al'umma muma mun kir-kiri (Azzahara relief foundation), domin taimakawa gajiyayyu da marassa karfi.
Yana da kyau dan'uwa na harka yasan wanene Haris, minene aikin Harisawa domin akwai yadda wasu na wajen harka da na cikin ke kallan mu suna mana wani gani na daban.
Wanene Haris ÷ Shi Haris ba Soja ba ne!, ba Dan sanda ba ne!, Haris ya bambanta da ko wane aiki, Aikin Harisanci aiki ne da ake bukatar wasu mutane majiya karfi masu jini ajika suyi na musamman dan tabbatar da Nizami domin tabbatar da wasu al'amirra wanda dole sai wasu sunyi babban yinkuri akan aikin, shi ne harisawa suyi.
Acikin Harka ne aka samu wasu Majiya karfi sike gudanar da aiyika kala daban-daban, Idan aikin Harisanci ya girma zai zamto yanada Janibobi daban daban, (Bangaren Kashe gobawa), (Bangaren Kiyaye Hadirran Hanya),(Bangaren Manoma), (Bangaren Kula da Lafiya), (Bangaren taimakon maras karfi), da sauransu.
Janibin Harisawa masu kashe gobara (fire servic), an kir-kiri wannan aikin ne lokacin da akayi gobara kusa damu Harisawa ne suka kashe gobarar sau dayawa hakan na faruwa, idan abin ya samu zai wice na 'yan kwana-kwanan hukuma nangaba insha Allah.
Janibin Harisawa masu kiyaye hadirran hanya (Traffic)÷ Janibi ne na kiyaye hadirran hanya ba irin na gwamnati ba domin na gwamnati wata hanyace ta samun makudan kudade, na gwamnati suna yatara ba aiki ba, namu na taimakon Al'umma ne.
Janibin Harisawa na Kiwan Lafiya na Harisawa ÷ Wannan shima wani janibi ne na kiwan Lafiya domin taimakawa Al'umma wajen kiyaye lafiyarsu.
Janibin Harisawa masu kula da taro ÷ shima wani Janibi ne na kula da dukkan Al'umma yayin da ake gudanar da taruka na Harka domin ganin anyi taron lafiya antashi lafiya, suna kula da masu hankoron kawo hari alokacin taron.
Janibin Harisawa masu Noma, wani Janibi ne wanda Harisawa suka kir-kira na Noma domin yanzu haka akwai gonar harisawa masu aiki bangaren sha'anin Gona.
Akwai ada din shekarun da idan Mutum ya yisu ya tashi daga aikin harisancin, domin Harisanci aiki ne na majiya karfi idan mutum ya tsufa saiya barma masu karfin, idan har Jahiliyya basu fahimci aikin Harisawa ba kai dan'uwa na Harka yakamata ka fahimci wanene Haris, minene aikin Harisawa.
Aikin Harisawa taimako ne ba abokan Hamayya ba!, in zakayi aiki kayi dan Allah yabo da suka kabar kowa da abinsa.
Sheik Ibrahim Zakzaky a Mu'utamar mai suna (Kyatata alaka tsakanin Harisawa da walikan 'yan uwa) idan kanaso kayiman magana ta WhatsApp in turoma 08166936199.
Tags:
Munasabobi