DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A.S )!!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Cikin kalamansa na hikima (A.S )yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KARAMCI SHINE BAYARWA BA A TAMBAYE KA BA, AMMA BAYARWA IDAN AN ROQE KA TA KAN ZAMA ABU BIYU, IMMA DAI DON SAMUN GIRMA KO DON GUDUN ZARGI .‘’
(NAHJUL-BALAAGHA )
Tabbas wannan magana haka take, domin duk wani abinda ka bawa wani ba tare da ya roqe ka ba ka fi jin dadi da samun nutsuwa cikin zuciyarka.
Amma yawancin abinda ake bayarwa bayan an roqe ka bai cika samun nutsuwa cikin zuciyar mai bayar da itan ba. Domin yawanci akan bayar ne don gudun kada a cewa mutum marowaci ne ko ba shi da kirki. Wani lokaci kuma sai wani abu (riya )ya shigo cikin zuciyar, wato ya bayar don a yabe shi kam cewa ai ba dama ka ace an roqe shi abu a rasa, hakan wai zai iya zama qasqanci gare shi.
A wani guri kuma (A.S )yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ BA A ZARGIN MUTUM MAI NACI WAJEN NENAN HAQQINSA, ABIN ZARGI SHINE MUTUMIN DA YA KARBE HAQQIM DA BA NASA BA.‘’
(NAHJUL-BALAAGHA )
Wannan magana ta wanke duk wani me fafutukar neman haqqinsa da ke hannun wani da ya riqe masa ko ya qwace masa.
Shi kuma wannan da ke riqe da haqqin wani ko ya qwace hakkin wani shine abin zargi wajen Allah ko da kuwa mutane ba su zarge shi ba.
Ka san su mutane ba kowanne daidai ne yake zama daidai a wajensu ba, sannan ba kowanne mummuna ne yake mummuna a wajensu.
SABODA HAKA A CIGABA DA NEMAN HAQQI 'YAN'UWA .
ALLAH NA TARE DA MASU GASKIYA .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~27th January , 2020.