Oyoyo Da Zuwan Sayyidah Ma'asumah (S.A)!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KOGIN DA KE FITAR DA LU'ULU'U DA MURJAANI

Bayan halittar Manzon Allah (S.A.W.W)da kuma qulla aure tsakaninsa da S ayyidah Khadijah (S.A )ba a taba yin wata halitta da qulla auratayya mai albarka kamar ta Sayyidah Fatimah  Ma'asumah (S.A)ba.

Dalili kuwa shine, halitta Manzon Allah da qulla aurensa da Sayyidah Khadijah (S.A )ne yayi sanadin haifar shugabar matan talikai .

Kuma ta hanyar hallitta shugabar matan talikai (S.A )aka sami sugabannin samarin gidan Aljannah (A.S ).

Sayyidah da Imam Ali(A.S )sun kasance tekuna biyu masu haduwa da juna ba tare da qetare iyaka ba.

Wannan bayani ya tabbata cikin Qur'ani inda Allah(T )ke cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ (Allah )YA GUDANAR DA TEKUWA BIYU (Imam Ali da Sayyidah Fatimah )SUNA HADUWA DA JUNA .

A TSAKANINSU (Ali da Fatimah )AKWAI WANI SHAMAKI (Manzon Allah  S.A.W .W )BA ZA  SU TABA QETAYE IYAKA BA (saboda Shi).

TO, DAGA WANNE CIKIN AYOYIN UBANGIJINKU KU KE QARYATAWA ?(wadannan tekuna ne ko kuma shamakin da ke tsakaninsu )?

LU'ULU'U DA MURJANI (Imam Hassan da Hussain (A.S )NA FITOWA DAGA GARE SU (Ali da Fatimah ).

TO, DAGA WANNE CIKIN AYOYIN UBANGIJINKU KU KE QARYATAWA?(Gwalagwalen da suka fito daga tsarkakekken tsatso )?

KUMA GARE SHI (Allah )AKWAI WASU JIRAGE (A 'imma (A.S ))DA YA SAMAR DASU CIKIN TEKUN KAMAR WASU MANYAN DUWATSU !

TO, DAGA WANNE CIKIN AYOYIN UBANGIJINKU KU KE QARYATAWA ?‘’

(Suratur-Rahman:19-25 )

Wadannan jirage sune A'imma iyalan gidan Manzon Allah (A.S ), duk wanda ya shige su ya tsira, wanda kuma ya qi shigarsu ya halaka.

YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU CIKIN WADANNAN JIRAGE.

👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

Daga wakilanmu na  Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-08126385470

~28th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post