Ko Kun San| Ayyukan Saɓon Da Suka Fi Wani Aikin Alherin!!!

DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A.S )!!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AIKIN SABON (sin )DA YA FI WANI ALHERIN

Cikin kalamansa na hikima (A.S )yana cewa;

‘’ AIKIN SABON DA KAYI (shi )DA NADAMA,YA FI AIKIN ALHERIN DA KAYI SHI DA FARIYA. ‘’

Tabbas, yana daga cikin sharadin tuba ga Allah yin nadama daga mummunan aikin da ka aikata. Duk wani aikin da ka aikata wanda Allah ya hane ka, sannan daga baya ka yi nadamar aikata wannan aiki, to, Allah na yin farin ciki da hakan.

Amma shi aikin alherin da ka aikata shi bisa fariya ko don ace lalle kai ma kaine, to, Allah ba ya buqatar wannan aiki naka komai kyawunsa.

Allah (T )na cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE ALLAH BA YA SON MAI FARIYA .‘’

A wata maganar tasa ta hikima (A.S )yana cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ JURE MASIFA JARUNTA CE, KAMUN KAI ARZIQI NE, TSARE KAI DAGA SABON ALLAH SHINE BABBAR GARKUWA !‘’

(NAHJUL-BALAAGHA )

Abinda wannan magana ta hikima ke karantar damu shine;

Babu wani jarimi fiye da mai jure masifar da ta same shi, ta hanyar jinya ce ko kuma ta hanyar jarrabawa da ya samu daga azzalumai ko kafirai . Sannan kuma duk wanda ya iya kame kansa daga kwadayin abin hannun wasu ko daga kwadayin duniya, to, ya sami babban arziqin da babu mai iya ba shi.

Tsare kai daga sabon Allah kuwa shine babbar garkuwa da ke shiga tsakaninka da wuta. Domin duk wanda ya nisanci sabawa Allah babu kokwanton shigarsa Aljannah .

YAA ALLAH KA BAMU IKON AIKI DA WADANNAN KALAMAI MASU ALBARKA .

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado Isah  Guda.

        08137925034

~28th January ,2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post