MUHAMMAD BN SALMAN, MAI JIRAN GADON SAUDIYYA, ZAI NEMI GAFARAR YAHUDAWA GAME DA YAKAR KHAIBAR DA ANNABI SAWW DA SAHABAI SUKA YI?
.
🇳🇬
MA, asuma Nigeria news update 🇳🇬
👉by sharhabil Usman pandoss
.
Ba wanda zai san yadda al'amura zasu kasance, a Saudiyya nan gaba, karkashin mulkin Muhammad Bn Salman, yarima mai jiran gadon mulkin kasar, wanda kuma yanzu a aikace shi ke mulki a kasar, saboda salon siyasar shi, ta fuskokin mulki, zamantakewa, tattalin arziki da ma addini, musamman saboda imamnin da ya ke da shi cewa wannan salon siyasar, shi zai dauwamar da mulkinsa tsawon shekaru 50 masu zuwa kamar yadda ya fada.
Ibn Salman kamar sauran sarakan alu Sa'ud, suna ganin Amurka ce silar dauwamar mulkinsu, ta yadda ba dan ita ba, da mulkinsu ko mako biyu ba zai kara yi ba, kamar yadda Donald Trump ya taba fada. Sai dai yarima Bin Salman, bayan ya kwace mukamin jiran gadon daga dan uwan ubansa, yarima Nayif, ya kuma kawo karshen dukkan sarakunan gidan, wadanda ya ke da shakku kan biyaiyarsu gare shi, ta hanyoyi daban daban, duk da haka, yana jin cewa dogaro ga Amurka kawai bai ishe shi ba, yana bukatar samun kusanci da kungiyar yahudawan Sahayuniya ta duniya, bisa zaton cewa sune babbar madogara a gare shi dan wanzuwar mulkinsa.
Wannan zumudin son hada kai da yahudawa, shi ya kai Muhammad Bn Salman ga yin watsi da yarjejeniyar zaman lafiyar da dan uwan ubansa Sarki Abdallah ya kulla da yahudawa a Bairut 2002, kan Palasyinu, inda ya yi wurgi da ita, dan gaggauta kawo karshen takaddama kan Palastinu, dake tsakanin larabawa da Isra'ila, dan samun damar kulla zumunci da yahudawan Sahayuniya na Isra'la, ba tare da wata matsala ba.
Muhammad Bn Salman shi ne mutum na farko daga cikin larabawa da ya taba budar baki rana tsaka, yace yahudawa fa suna da hakki a cikin kasar Palastinu, kuma ya zama dole Palastinawa su yarda da wannan hakki na yahudawa. sa'annan shi ne na farkon wanda ya aiyana kungiyoyin gwagwarmayar Palastinu a matsayin yan ta'adda, sannan ya tattara kafofin yada lanaran kasarsa yasa, suka rika tallata Isra'ila a matsayin kasa ce abokiyar zama, wadda ya zama dole a karbe ta a wannan yankin.
Shi ne kuma wanda ya amince wasu jami'an gwamnatinsu, irin su janar Anwar Ishqi, da yarima Turki bn Faisal, su ka kai ziyara Isra'ila, har suka gana da wasu jami'an gwamnati, da nufin kulla alakar tsaro da ta siyasa da yahudawa. A hannu daya kuma, ya zare takobin fada da duk wasu masu nuna tausayawa ga Palastinawa, hatta a shafukan sadarwar intanet, haka ma ya shata daga da kungiyoyin gwagwarmaya masu fada da kasantuwar Isra'ila a yankin.
Kwanan nan, da ya rage saura kwana biyu, Donald Trump ya yi shelar baiyana abinda ake kira 'Safqatul Qarn' wani shirin kawo karshen gwagwarmayar yanto Palastinu da tabbatuwar kasar Isra'ila, wanda shiri ne da bai samu tabbata ba, in ba dan su Ibn Salman sun bada hadin kai da amincewa zasu sayar da kasar Palastinu kan dala Biliyan hamsin ba, a wani taron da suka kira na tattalin arziki, wanda suka yi a kasar Bahrai a shekarar da ta wuce, wanda surikin Trump Jarud Kushna, da wasu yahudawan suka halarta.
A dai wannan lokacin dai har wala yai, sai ga wani ayari daga tashar talabijin ta Isra'ila, mai suna 'channel 12' sun dira cikin kasar Saudiyya, har da gabatar da shirin musamman mai suna 'Dan Isra'ila a Saudiyya', wanda ya kunshi tattaunawa da mutane daban daban a biranen Saudiyyar da suka hada da Madina, Riyad da Jidda.
Kafin wannan yarjejeniya ta Trump da kwana biyu, dai har wala yau, sai ga ministan cikin gidan Isra'ila Aryiih Dar'ii ya rattaba hannu kan wani shiri, da zai baiwa yahudawa damar ziyartar Saudiyya a karo na farko cikin tarihi, kamar yadda jaridar Haaretz ta nakalto, inda wannan zai bada dama ga yahudawa su je ziyarar ibada zuwa Saudiyya lokacin hajji da umara.
Kafin kwana biyu da shelar ta Truml dai har wala yau, sai ga jaridar 'Times of Isra'il' ta fitar da wani rahoton ta cewa nan ba da dadewa ba, yahudawa zasu samu damar shiga Saudiyya, har ma su ziyarci wurarensu na tarihi da ke can, kamar kwarin Khaibar.
Yahudawan dai sun kirga wurare biyar da suka ce nasu ne a tarihi, wadanda suke cikin Saudiyyar a yanzu. Wurare kuwa sune:
1. kwarin Khaibar, wanda wuri ne mafi kyan dausayi a yammacin Saudiyya.
2. Badalar Khaibar, wadda rahoton ya nuna cewa mallakar yahudawa ce, amma Annabi Muhammad SAWW da sahabbansa suka kwace shekara 1400 da suka shude, inda Ali bn Abi Talib, da hannunsa ya balle kyauren kofar ya jefar.
3. Fadar sarkin yahudawan Khaibar, wadda suka ce tana cike da gwala-gwalai, da kayan kudi iri-iri.
4. 'Teema'a' wanda ita ma birni ce mai katanga ta yahudawa,
5. 'Rijiyar Hudaj' da ke Teema'a din, wadda tarihin ta ya kai shekara 2500, wadda mallakar wani bayahude ce.
Abu mafi muhimmanci a wannan rahoto shi ne, yadda rahoton ya yi amfani da kalmomi kamar "wanda asali mallakar yahudawa ne" da kuma "tana cike da gwala-gwalai da kayan kudi" da kuma "kasa ce mafi kyawun Dausayi"
Irin wadannan kalamai, ko shakka babu an fade su ne da manufa, wadda gwamnatin Isra'ila ke da nufin ganin ta cimmata komi tsawon lomaci, a cikin mulkin Muhammad bn Salman, matukar shi ke kan mulki. Kuma wadannan hakkoki ba wai Isra'ila zata nemi a biya ta diyyarsu bane kawai,a'a wurare din zasu nemi su karbi kayansu, su maida su bangaren daular Urshalima da suke mafarkin kafawa.
Kuma bamu taba zaton yadda Bn Salman ya makance da son gadon sarautar Saudiyyar nan, na tsawon shekara 50, kamar gadda ya tsarawa kansa, zai hana yahudawan duk abinsa suka nema, ciki ko har da neman gafarar shugaban yahudawa Binyamin Natenyahu, game da abinda Annabi Muhammad SAWW da sahabbai suka aikata, na yakar Khaibar da kwace ta daga yahudawa, bayan ya amince a yiwa al-qur'ani kwaskwarima.