Sayyeed Zakzaky Yake Fada A Wajen Gasar Faretin 'Yan Fudiyya A Hussainiyyah.

Daga Wakilin Mu --Idishia Jos. Yanzu kuma ga wasu abubuwa da ya fito a Handset su yi ta wasanni, in kaga yazo ya karbi Handset sai yai ta wasa a ciki yayi ta Game ya matsa wannan ya bugi nan wannan ba karatu bane ba kuma ilimi bane. Sam kada mutum ya yarda da wani Game! Game mummunan abu ne. Sam bai kamata mutum yayi wani game ba, koda na rahane akwai wasannin raha wanda suke da amfani Game bai da wani amfani. In kana son ka yi wasa mai amfani shine ka dan yi wanda zaka motsa jikin ka, wanda jikin ka zai dan ji. Ka dan zuba a guje kaje can ka dawo to, wannan yana da kyau ko ka hau doki, ko kuma ayi tsere kamar wannan Faretin don shine wasan da zai yi amfani a jikin ka Amma Game bai da amfani Game din Handset bata maka lokaci zai yi, lokacin da ya kamata kayi karatu in kana Game, in Game din ya dauke hankalin ka sai ya zama Game din kake tunani in an tambaye ka wani abu ana magana a aji kai kana tunanin in wannan abin ya bugi wannan ya za'ayi wannan yayi sama in wannan yayi kasa ya za'ayi wannan yayi kaza. Kai kuma baka san mai ake ba a ajin, wasu ma akan same su dashi a aji suna mammatsawa yana 'tsitsi' akan kwace a makarantu. To, shi Game ba abin kirki bane Sam sabida haka shi ba wasa bane da ya kamata mutum yayi ba Sam Sam ballantana wasu Ba'a din wasanni ba bukatansu samsam, saboda haka ku sa hankali akan abinda ake koya muku "Kuyita Karatu-Kuyita Karatu-Kuyita Karatu". Ba tsayawa kuyitatayi insha Allahul-Azeem nan gaba kuma za a ga amfanan karatun. Nasan karatu lallai a gaskiyar magana ba yana da dadi bane amma amfanin sa yana da dadi kuma ba yadda za'ayi kaci gajiyar karatu in baka yi ba. Shi wani abu ne da ba'a mishi wayo kenan, ba'a ma karatu wayo yanzu kasar nan ta cika da wadansu irin mutane makil wai zasu ma karatu wayo sai suka rai na addinin musulunci sai kowanne ya zama shi Sheikh, zaku ta jin su a Radiyo ne a ina ne kowanne yana bada labarin addini kowa ya zama Sheikh Sheikh Sheikh, Sheikh ko kuma Sharks?. Wannan irin irin kifin nan mai fadan tsiya nan a ruwa. To, shikke nan sai kaji kowanne ya yana koyarwar da addini, bai yi karatu ba ai ba'a ma karatu wayo duk wanda ka Ganshi da karatu ya wahala ne, kuma ba'a samun karatu da dabara wahala ake sha karanta tarihin duk Malaman duk duniya kaji ba wani Malamin duniyanan da bai wahala ba ka karanta kaji. Saboda haka shi wannan ka'idansa sane Sabida haka kada kace akwai wani wayo da zaka yi ma karatu sai a samu ilimi, aa aiki ake tukuru sannan asha wahala sannan a samu karatu sai aci gajiyansa. Wanda kaga sun haskaka duniya sun amfana sun anfamar kuma ana amfani da ilimin su to wadan nan sune suka bautawa ilimi kenan. Wadan nan su Sheikh, Sheikh, din nan kwana Biyu za'ayi bari dasu a juji a juye su Sai tarihi, dasu da basu duk daya. Basu amfana ba basu amfanar da kowa ba surutu ne Anje an sassa Sifiku anyi ifface ifface amma bashi ne ilimi ba ba kuma zai taba amfanar da kowa ba. Koda yake wata kila ana basu abin sawa a baka dama dai sun bari ma da ya wuce da yafi musu alheri, to insha Allah Azeem da fatan mun anfama muna fatan nan gaba muga abinda zamu gani yafi abinda muka gani yanzu muna rokon Allah ya amfani yaran mu ya kyautata tarbinsu ya sa biyayya a zukatansu kamar yadda muke rokon Allah yasa kunya a zukatan matan mu da tausayi akan zukatan iyaye da magidanta da manya kuma Allah (T) ya taimake mu da taimakonsa ya kare mu da kariyansa ya nuna mana na badi dana shekaru masu zuwa. Jawabin Sheikh Zakzaky (H) shekaru baya da suka gabata wanda aka yi Gasar Fareti 'Yan Fudiyya na karshe a cikin Hussainiyyah kafin a fara yi a cikin filin Polo.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post