
Daga Wakilin Mu --Idishia Jos.
A ranar Asabar ne ma’aikatar lafiyar jihar Kaduna ta tabbatar da barkewar cutar nan na zazzabin Lassa a jihar Kaduna, an samu wani matashi ne mai shekara 36 da haihuwa Chikun dauke da cutar bayan da aka yi masa gwaje gwajen asibiti. Kwamoshinna lafiya na jihar Kaduna, Amina Baloni, ta bayar da wannan sanarwa, in da tace wanda ake zargi da kamuwa da cutar a hakin yanzu an kebe shi a wuri na musamman inda ake yi masa magani tare da jinyarsa.
Ma’aikatan lafiya na kara jaddada kiran da take yi ga al’umma da su kula da tsafta da kuma lafiyar jikinsu tare da kuma gaggauta kai rahoton duk wani lamarin da basu gane ba a cibiyar samar da lafiya na kusa da su. “Gwaji da aka yi ya tabbatar da cewa, matashin dan shekara 36 yana dauke da cutar zazzabin lassa, tuni kuma aka kebe shi cibiya na musammna na kula da masu fama da cutar don kare yaduwarsa ga sauran al’umma.
“Ma’aikatan lafiya ta samar da dukkan magungunan da ake bukata a cibiyoyin kula da marasa lafiyar kuma jami’anmu na cikin shirin fuskantar duk barkewar cutar da aka samu a na gaba.
Jami’an mu na musamman na cikin shirin kota kwana an kuma sanya sauran asibitoci a cikin ko ta kwana ta yadda za su gaggauta muka duk wani da aka tabbatar day a kamu da cutar zuwa cibiyar da aka kebe na musamman don kula da masu cutar. “Muna kuma kira ga al’umma das u tabbatar da cikakken tsaftar jikinsu da kuma wuraren zamansu su kuma tabbatar da suna ajiye kayan abinci a wuraren da yakamata, su kuma kai rahoton du wani lamarin da zai nemi barana ga kiwon lafiyarsu ga cibiyoyin lafiya day a kamata. “Ana kuma iya mika rahoton duk wani barkewar cutar ga jami’a na musaman a kan wannn lambobin 0803645755 ko kuma 08027396344”, injita.
Sama da jihohi 12 ne ake sa tsammanin wannan cutar ta bayya.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates