KWANA 1500 KENAN ANA CIGABA DA TSARE SHEIKH ZAKZAKY (H)




Cigaba da tsare jagoran Harkar musulunci Sheikh Zakzaky (H) da gwamnatin Nigeria keyi Babban Zalunci ne. Wanda hakan yake nunawa a fili irin makircin ma'kiya Addinin Musulunci ne wajen kokarin da sukeyi na rushe Addini.

Wannan cigaba da tsare Sheikh Zakzaky da gwamnatin Nigeria keyi tun bayan waki'ar data auku a Zaria a watan December shekara ta 2015, Ta yadda sojojin Nigeria suka aukawa Sheikh Zakzaky a Gidansa dake unguwar Gyallesu, Wanda ta sanadiyyar hakan sojoji suka kashe 'ya'yansa guda uku wato:-

Shaheed Sayyid Hammad
Shaheed Sayyid Aliyu Haidar Da kuma Dan autansu
Shaheed Sayyid Humaid

Duk cikarsu 'ya'yan Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) ne, kuma akan idonsa aka kashesu, Wannan wani irin Zalunci ne.

Bayan sun Harbi Sheikh Zakzaky (H) da bindiga a wurare Daban-Daban a sassan jikinsa, Sannan Gwamnatin Nigeria ta tsareshi tare da matarsa Malama Zeenatuddeen, Wacce itama Sojoji suka harba da bindiga.

Kuma har yanzu sama da Shekara hudu kwana 1500 kenan suna tsare dasu Wanda da suna wajen DSS amma izuwa yanzu sun mayar dasu kidan yarin Kaduna, kuma har yau Gwamnatin Buhari ta hana Sheikh Zakzaky (H) ya samu kulawar lafiyarsa daga likitocin da suka dace.


Sai dai Allah Subhanahu wa ta'ala yayi Alkawarin zai kare addininsa, kuma zai rika baiwa muminai nasara a kan makiyansu, ta yadda ma'abota Addini zasuyi rinjaye.

Da wannan nake ce muku Bissalam daga Dan Dan'uwanku Aminu Abdullahi Danmagina, Ku kasance da Ma'asumah Nigerian News Update Shafi domin kai da iyalinka.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post